Da Ɗumisa: Shugaba Buhari Zai Tafi Ghana a Ranar Lahadi

Da Ɗumisa: Shugaba Buhari Zai Tafi Ghana a Ranar Lahadi

- Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari zai tafi kasar Ghana a ranar Lahadi 30 ga watan Mayu

- Shugaba Buhari zai tafi Ghana ne don hallartar taron ECOWAS da aka kira don tattaunawa kan halin da Mali ke ciki

- Wadanda za su yi wa Shugaba Buhari rakiya sun hada da Ministan Harkokin Kasashen Waje, Ministan Tsaro da sauransu

Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar Lahadi domin zuwa Accra, Ghana inda zai hallarci taron gaggawa na kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, da za a yi don tattauna kan rikicin siyasar kasar Mali.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya sanar da tafiyar shugaban kasar cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Channels Tv ta ruwaito.

Da Dumisa: Buhari Zai Tafi Ghana Saboda Rikicin Kasar Mali
Da Dumisa: Buhari Zai Tafi Ghana Saboda Rikicin Kasar Mali. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano

Ana sa ran shugaban na Nigeria zai dawo gida "a karshen taron na kwana daya."

A cewar Adesina, shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ne ya kira taron.

Kafin kiran taron, Buhari ya gana da jakada na musamman kuma mai sulhu a Mali, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya yi masa bayani game da abubuwan da ya tattauna da manyan yan siyasa a Mali.

"A yayin da lamura ke cigaba da sauyawa a Mali, Nigeria ta yi tir da juyin mulkin da aka yi a ranar 24 ga watan Mayu, da tsare shugaban kasa da farai minista da sojoji suka yi, tana mai kira da cewa a saki dukkan fararen hula da ake tsare da su," sanarwar ta kara da cewa.

KU KARANTA: Masu Zanga-Zanga Sun Tafi Da Gawarwaki Zuwa Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara

"Wadanda za su yi wa Shugaba Buhari rakiya sun hada da ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi, Ministan Kasuwanci da Saka Hannun Jari, Otunba Richard Adebayo da Shugaban NIA, Ahmed Rufai Abubakar."

A wai labari daban, Hukumar Kiyayye Hadura Ta Kasa, FRSC, ta ce mutane hudu sun rasu yayin da wasu hudu sun jikkata sakamakon hatsarin mota da ta faru a kauyen Wailo, karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi a ranar Alhamis, Vanguard ta ruwaito.

Mr Yusuf Abdullahi, Kwamandan hukumar na Bauchi, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai ta kasa, NAN, a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel