Mummunan Hatsarin Mota Ta Halaka Rayuka Huɗu a Jihar Bauchi

Mummunan Hatsarin Mota Ta Halaka Rayuka Huɗu a Jihar Bauchi

- Hatsarin mota ya yi sanadin rasuwar mutane hudu a Darazo a jihar Bauchi

- Shugaban hukumar FRSC reshen jihar Bauchi, Mr Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan

- Yusuf Abdullahi ya ce gudu na ganganci da obatekin ne ya janyo hatsarin

Hukumar Kiyayye Hadura Ta Kasa, FRSC, ta ce mutane hudu sun rasu yayin da wasu hudu sun jikkata sakamakon hatsarin mota da ta faru a kauyen Wailo, karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi a ranar Alhamis, Vanguard ta ruwaito.

Mr Yusuf Abdullahi, Kwamandan hukumar na Bauchi, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai ta kasa, NAN, a ranar Juma'a.

Mummunan Hatsarin Mota Ta Halaka Rayuka Huɗu a Jihar Bauchi
Mummunan Hatsarin Mota Ta Halaka Rayuka Huɗu a Jihar Bauchi. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA

Abdullahi ya ce gudu fiye da kima da obatekin ne ya yi sanadin hatsarin da ya faru misalin karfe 2.45 na yamma kamar yadda Independent ta ruwaito.

A cewarsa dukkan mutanen da hatsarin ya shafa maza ne kuma manya.

"An kai gawarwakin mutanen hudu da suka mutu a hatsarin zuwa babban asibitin Darazo," in ji shi.

Ya kuma ce wadanda suka jikkata suna nan a asibitin na Darazo ana musu magani sakamakon cetonsu da jami'an na FRSC suka yi.

"Hatsarin ya faru ne tsakanin mota Volkswagen Saloon Golf mai lamba MUB739QW da motar haya kirar Toyota Matrix eagon mai lamba BEN256TA mallakar kungiyar direbobi na kasa NURTW.

"Jami'an mu, Zebra 45, sun yi bajinta domin sun isa wurin da hatsarin ya faru cikin gaggawa.

"Muna da motoccin bada taimakon gaggawa ta kai mutane asibiti a wurare daban-daban domin irin hakan.

KU KARANTA: An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati

"An ajiye su domin su bada taimako da ceto idan anyi hatsari. Sun isa wurin sun kai su asibiti, wadanda suka tsira suna samun sauki a asibiti," in ji shi.

Shugaban na FRSC ya gargadi mutane su rika kiyayye dokokin tuki musamma yawan gudu domin gudun ne ke janyo kimanin kashi 90 cikin 100 na hatsari a kasar.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel