Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano

Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano

- Jami'in hukumar FRSC a Kano ya hadu da ajalinsa bayan tare wani direban babban mota

- Wani da lamarin ya faru a idonsa ya ce jami'an na FRSC sun tsayar da direban suna bincikar motarsa sai suka tunkuda jami'in suka tsere

- Mai magana da yawun hukumar FRSC a Kano, Muhammad Mu'awiyya ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce jami'in ya kama direban da laifi kafin ya tsere

Wani direban babban mota da ba a san ko wanene ba ya kashe jami'in hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC, a kan babban titin Hotoro ring - road a jihar Kano, Vanguard ta ruwaito.

An gano cewa lamarin ya faru ne a yayin da jami'in na FRSC ya yi yunkurin bincika babbar motan.

Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano
Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu Zanga-Zanga Sun Tafi Da Gawarwaki Zuwa Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara

Wani shaidan ganin ido mai suna Abubakar Abubakar ya ce an turo jami'in ne ya fado kasa a yayin da ya ke duba motar kamar yadda Nigerian Tracker ta ruwaito.

"Jami'in na FRSC na kokarin ya tsayar da direban babban motar, da ya tsaya daya daga cikin jami'an ya rike madubin gefe na motar sai daya daga cikin yaran ya tunkuda shi ya fadi kasa suka gudu."

KU KARANTA: Nigeria Ba Za Ta Taɓa Zama Ƙasar Musulunci Ba, Inji Jikan Shagari

Jami'in hulda da jama'a na hukumar FRSC reshen jihar Kano, Mr Muhammad Mu'awiyya wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce jami'in ya kama shi da saba dokar tuki ne kafin ya tsere.

A wani labarin rahoton daban, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito. Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: