Masu Zanga-Zanga Sun Tafi Da Gawarwaki Zuwa Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara

Masu Zanga-Zanga Sun Tafi Da Gawarwaki Zuwa Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara

- Wasu mutane a garin Zurmi da ke karamar hukumar Zurmi a Zamfar sun yi zanga-zanga kan kashe su da yan bindiga ke yi

- Masu zanga-zangar sun dauki wasu gawarwakin mutane da yan bindigan suka kashe a harin da aka kai musu a baya-bayan nan sun tafi gidan sarki

- Sai dai koda suka isa fadar sarkin bai fito ba inda aka ce yana cikin gidansa sannan suka yi kone-kone kafin barin fadar sarkin

Zanga-zanga ta barke a safiyar ranar Juma'a a garin Zurmi, hedkwatar karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara saboda yawaitar hare-haren yan bindiga da ke kashe mutane a garuruwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mutane da dama sun rasa rayyukansu wasu daruruwan sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren yan bindiga da ya ki-ci ya-ki-cinyewa a garuruwan jihar.

Masu Zanga-Zanga Sun Kai Gawarwaki Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara
Masu Zanga-Zanga Sun Kai Gawarwaki Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA

A makon da ta gabata, yan bindiga sun kai hari a wani gari a karamar hukumar Zurmi inda suka kashe fiye da mutane 11.

Mazauna garin sun shaidawa majiyar Legit.ng garuruwa da dama a yankin na fuskantar barazana daga yan bindiga.

Sun dauko wasu gawarwakin sun shiga gari suna zanga-zanga nuna damuwarsu kan hare-haren da yan bindiga ke kai musu.

Wani daga cikin mazauna garin da ya ce sunansa Mustapha ya ce: "Suna hanyarsu zuwa fadar sarki domin gabatar da kokensu.

"Sai dai, Sarkin bai fito ya gana da su ba domin an ce yana cikin gida. Sun yi kone-kone a kafin suka tafi.

"Masu zanga-zangan sun bar fadar sunnan suka hadu a hanyar Gusau zuwa Jibia suka fara fasa motoccin matafiya da ke bin titin.

DUBA WANNAN: Sojoji Sun Ragargaji 'Yan IPOB, Sun Kashe 7 Sun Kama Biyar a Rivers

"Sun kuma fasa gilasan motoccin da aka ajiye a gefen titi."

"Yanzu abubuwa sun dai-daita a yayin da jami'an tsaro ke sintiri a titunan garin domin tabbatar da doka da oda.

"Sannan mutane sun koma sun cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba," in ji shi.

An yi kokari ji ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu amma ba a same shi ba a yayin hada wannan rahoton.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel