Da Ɗumi-Ɗumi: Tawagar Goodluck Jonathan Ta Gana da Shugaban Ƙasar Mali da Aka Hamɓarar
- Tawagar wakilan ƙungiyar kasashen nahiyar Afirka ECOWAS ta gana da hamɓararren shugaban Mali da Firaminista
- Shugaban Mali da Firaminista sun shaida wa wakilan ECOWAS ɗin sun yi murabus daga kan muƙamansu
- Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa sojoji ne suka tilasta musu yin murabus ɗin bawai don son ransu bane
Tawagar wakilan ƙungiyar ƙasashen nahiyarAfirca ECOWAS ta gana da tsohon shugaban ƙasar Mali, Bah Ndaw, da sojoji suka kifar tare da Firaminista.
KARANTA ANAN: Ya Kamata a Baiwa Jihohi Damar Yanke Kananan Hukumomi Nawa Zasu Iya Ɗauka, El-Rufa'i
Tawagar wakilan ƙarƙashin jagorancin Dr. Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban ƙasar Najeriya ta gana da shugaban ne biyo bayan hamɓarar da shi da sojoji suka yi ranar Litinin..
A lokacin ganawar tasu, shugaban Mali da Firaminista sun bayyana aje muƙamansu ga wakilan ECOWAS ɗin.
Rahoton da BBC ta ruwaito ya nuna cewa sojoji ne suka tilasta wa shuwagabannin biyu dole su sauka daga kan muƙamansu.
Kanal Assimi Goita, Sojan da ya shugaban ci hamɓarar da gwamnatin ƙasar a shekarar da ta gaba ta ya bada sanarwar tsige shugaban ƙasa da Firaminista ranar Talata.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Sheƙe Yan Bindiga 5, Ta Damƙe 16 a Jihar Katsina
Kanal ɗin yace yana zargin su da naɗa sabbin ministoci a gwamnatin rikon ƙwarya ba tare da tuntuɓar ɓangaren sojojin ba.
A halin yanzu ƙungiyar ECOWAS da takwararta da Turai na duba yuwuwar sanya takunkumi ga sojojin da suka jagoranci juyin mulkin.
Ana sa ran, yau kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya zai zauna ya tattauna kan rikicin siyasar ƙasar Mali.
Idan baku manta ba, Legit.ng hausa ta kawo muku rahoton cewa sojoji a Mali sun tsare shugaban ƙasar da Firaminista.
Rahoton channels tv ya nuna cewa an fara rade-radin juyin-mulki a kasar Mali tun a ranar Talata, bayan da aka fahimci cewa sojoji sun kama shugabannin kasar, sun tsare su.
A wani labarin kuma Mako Ɗaya Bayan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru, Rundunar Soji Ta Shirya Gagarumin Bikin POP
Rundunar sojin ƙasa zata gudanar da bikin yaye sabbin sojoji 80 da aka saba yi ranar 29 ga watan Mayu.
Rundunar ta ɗage bikin ne da aka shirya za'a yi a baya saboda mutuwar shugaban rundunar, Janar Ibrahim Attahiru.
Asali: Legit.ng