Mako Ɗaya Bayan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru, Rundunar Soji Ta Shirya Gagarumin Bikin POP
- Rundunar sojin ƙasa zata gudanar da bikin yaye sabbin sojoji 80 da aka saba yi ranar 29 ga watan Mayu
- Rundunar ta ɗage bikin ne da aka shirya za'a yi a baya saboda mutuwar shugaban rundunar, Janar Ibrahim Attahiru
- Attahiru tare da wasu manyan jami'an soji sun rasa rayuwarsu ne a wani hatsarin jirgi da ya rutsa da su a Kaduna
An ɗage bikin yaye sabbin sojoji da aka saba yi zuwa 29 ga watan Mayu biyo bayan mutuwar shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Ibrahim Attahiru.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Yi Ram da Jami’in Soji Kan Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa
Attahiru, tare da manyan jami'an soji sun rasa rayuwarsu ne a wani hatsarin jirgi da ya rutsa da su ranar Jumu'a a Kaduna.
Capt. Audu Arigu, mataimakin daraktan yaɗa labarai na defot ɗin soji, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Da farko an saka ranar 22 ga watan Mayu a matsayin ranar bikin yaye sabbin sojin, kuma shugaban sojin shine babban baƙo a wurin taron.
Hakanan kuma an tsara cewa, Janar Attahiru, shine zai ƙaddamar da sabuwar cibiyar duba lafiya da aka gina a defot ɗin, a wani ɓangare na bikin.
KARANTA ANAN: Bayan Mutuwar COAS Attahiru, FG Ta Bayyana Ranar da Wasu Sabbin Jirgaen Yaƙi Zasu Iso Najeriya
Cpt. Arigu yace yanzun za'a gudanar da bikin yaye sabbin soji (POP) ranar 29 ga watan Mayu, kamar yadda guardian ta ruwaito.
Arigu yace: "Bikin yaye sabbin sojin ɗaya ne daga cikin ayyukan da ake yi domin nuna an kammala horad da jami'ai yadda ya kamata, kuma horon ɗaya ne daga cikin matakin zama soja. Yana nuna kololuwar horon jami'in soji da biyayyarsa.
A wani labarin kuma Taɓarɓarewar Tsaro: CUPP Ta Buƙaci Shugaba Buhari Yayi Murabus
Haɗakar jam'iyyun siyasa CUPP, sun yi kira ga shugaban ƙasa Buhari yayi murabus daga kujerar domin gwamnatinsa ta gaza,.kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Shugaban kwamitin yaɗa labarai na CUPP, Chukwudi Ezeobika, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a Abuja.
Asali: Legit.ng