Ya Kamata a Baiwa Jihohi Damar Yanke Kananan Hukumomi Nawa Zasu Iya Ɗauka, El-Rufa'i
- Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i, yace kamata yayi a baiwa gwamnonin jihohi damar yanke yawan kananan hukumomin da zasu iya ɗauka
- Gwamnan yace idan akace za'a maƙala wa gwamnatin tarayya dukka ƙananan hukumomin ƙasar nan to an saɓawa tsarin mulkin jamhuriya
- El-Rufa'i ya faɗi haka ne a wajen ji ta bakin jama'a akan kudirin gyara kundin tsarin mulkin ƙasar nan da yan majalisa suka shirya
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, yace jihohi ne ya kamata su yanke kwatankwacin yawan kananan hukumomin da zasu iya ɗauka.
KARANTA ANAN: Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Ɗan Sanda, Sun Bankawa Motar Sintiri Wuta
Gwamnan yace Najeriya ƙasa ce dake ɗauke da gwamnatocin jihohi 36 da kuma gwamnatin tarayya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A cewar gwamnan, a lissafo jerin kananan hukumomin ƙasar nan 774 sannan ace ana son maƙala wa gwamnatin tarayya su kai tsaye, wannan ya saɓa wa tsarin mulkin da muke tafiya a kanshi na jamhuriya.
El-Rufa'i yayi wannan jawabi ne a wurin jin ta bakin al'umma kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar nan a ranar Laraba.
El-Rufa'i yace "Kamata yayi a bar kowace jiha ta yanke adadin yawan ƙananan hukumomin ta waɗanda zata iya samar wa kuɗaɗe kwatankwacin kuɗin shigarta, hakan zai sa a gudanar da gwamnati mai kyau kuma cikin adalci."
KARANTA ANAN: Daga Ƙarshe, FG Ta Faɗi Matsayarta Kan Kudirin Soke Bautar Ƙasa NYSC
"Kowace jiha ita ya kamata ta duba ta ga tsarin yadda take son kananan hukumominta su kasan ce, amma dai abunda ake so shine a sanya tsarin demokaraɗiyya a cikin kowane tsari."
"Kuma a baiwa kowace jiha lokacin gudanar da zaɓen ƙananan hukumominta amma kar ya wuce tsawon shekaru huɗu a tsakani."
A wani labarin kuma Mako Ɗaya Bayan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru, Rundunar Soji Ta Shirya Gagarumin Bikin POP
Rundunar sojin ƙasa zata gudanar da bikin yaye sabbin sojoji 80 da aka saba yi ranar 29 ga watan Mayu.
Rundunar ta ɗage bikin ne da aka shirya za'a yi a baya saboda mutuwar shugaban rundunar, Janar Ibrahim Attahiru.
Asali: Legit.ng