Wani tsohon shugaban ƙasa zai mutu tsakanin watan Yuni da Yuli, babban limamin coci ya nemi a dage da addu’a

Wani tsohon shugaban ƙasa zai mutu tsakanin watan Yuni da Yuli, babban limamin coci ya nemi a dage da addu’a

- An bukaci ‘yan Najeriya da suyi addu’a domin kaucewa yawan mace-mace a kasar

- Babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu mutane 10, sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama a ranar Juma’a, 21 ga Mayu

- Sai dai kuma, Apostle Paul Okikijesu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi addu’a kan mutuwar wani tsohon shugaban

Wani rahoto da Sahara Reporters ta fitar ya nuna cewa wani malamin cocin Christ Apostolic Miracle Ministry, Apostle Paul Okikijesu, ya yi hasashen cewa Najeriya na iya fuskantar mutuwar manyan mutane a hatsarin jirgin sama tsakanin watan Yuni zuwa Yulin 2021.

Legit.ng ta tattaro cewa saboda haka, malamin ya bukaci yan Najeriya da suyi addu’a don kauce wa masifar da ke tafe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Gwamna El-Rufai ya tsige masu mukaman siyasa 19

Wani tsohon shugaban ƙasa zai mutu tsakanin watan Yuni da Yuli, babban limamin coci ya nemi a dage da addu’a
Wani tsohon shugaban ƙasa zai mutu tsakanin watan Yuni da Yuli, babban limamin coci ya nemi a dage da addu’a Hoto: Paul Okikijesu
Asali: Facebook

Okikijesu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, wanda ya bayyana hasashen.

Ya ce:

“Haka Ubangiji ya ce: Ni Ubangiji na riga na umarci mutane da su yi addu’a a kan hatsarin jirgin sama da gobara ko hatsari a filayen jiragen sama; wani jirgi mai zaman kansa na iya faɗuwa wanda zai haifar da asarar rayuka; idan mutane basu dage da addu’a ba. Ku yi addu'a kan haɗarin jirgin saman jirgi mai zaman kansa tsakanin Yuni zuwa Yuli 2021."

Okikijesu ya kuma roki ‘yan Najeriya da suyi addu’a game da mutuwar wani tsohon shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Juyin-mulki: Najeriya ta yi magana da babbar murya, ta gargadi Sojojin Mali su shiga taitayinsu

Ya kuma bayyana ce tsoffin gwamnoni wadanda yanzu suke rike da mukaman sanatoci za su gamu da hukuncin Allah.

A wani labari, wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna, Alhaji Muhammadu Murtala ya ce shawarar da jam’iyyar ta yanke na bude tikitin takararta na shugaban kasa a 2023 ba zai shafi kudirin shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba.

Tinubu, babban jigon jam’iyya mai mulki ta APC na kasa na daya daga cikin wadanda ke kan gaba wajen neman tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Murtala, babban mai goyon bayan Tinubu a yankin arewa maso yammacin kasar, ya yi wannan bayanin ne yayin tattaunawa da jaridar Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel