Sojojin Mali Sun Tsare Shugaban Ƙasa, Farai Minista Da Ministan Tsaro

Sojojin Mali Sun Tsare Shugaban Ƙasa, Farai Minista Da Ministan Tsaro

- Dakarun Sojoji a kasar Mali sun kama Shugba Ndaw, Farai Minista Ouane da Ministan tsaro Doucoure a Mali

- Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun tsare mutane ukun ne a wani wuri a wajen babban birnin ƙasar Bamako

- A halin yanzu ba a tabbatar da ainihin abin da sojojin ke nufi da kama su ba sai dai ana hasashen ba zai rasa nasaba da kafa sabuwar gwamnatin farar hula a kasar ba

Sojojin ƙasar Mali sun tsare Shugaba Bah Ndaw, Farai Minista Moctar Ouane da ministan tsaro Souleymane Doucoure a ranar Litinin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Hakan na zuwa ne a yayin da rikicin siyasa ke ƙara ƙamari a ƙasar watanni bayan sojoji sun hamɓarar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar.

Sojojin Mali Sun Tsare Shugaba Ƙasa, Farai Minista Da Ministan Tsaro
Sojojin Mali Sun Tsare Shugaba Ƙasa, Farai Minista Da Ministan Tsaro. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi

An tafi da mutane ukun wani sansanin sojoji da ke wajen babban birnin kasar Bamako, awanni biyu bayan mutum biyu cikin sojoji biyu sun rasa muƙamansu a wani sauye-sauye da ake yi a gwamnati, a cewar majiyar diflomasiyya da gwamnati.

An ɗora wa Ndaw da Ouane alhakin sa ido kan yadda za a mayar da mulkin ƙasar hannun farar hula a cikin watanni 18 bayan juyin mulki a watan Agusta amma akwai alamun ba su aikata abin da sojojin ke so game da wasu muhimman batutuwa.

KU KRANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Kofar Gidanta

Ba a san ainihin abin da sojojin ke nufi a yanzu. Wani jami'in soja ya ce wannan ba kame bane. "Abin da suka yi ba shi da kyau," in ji majiyar

A wani labarin rahoton daban, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito. Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel