Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi

Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi

- Mutanen garin Gauraka a jihar Niger sunyi zanga-zanga sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna domin janyo hankalin hukuma ta taimaka musu

- Mutanen sun tare titin suna kona tayoyi wadda hakan ya janyo cinkoson ababen hawa a kan titin

- Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce kimanin mutum 30 ne yan bindiga suka sace a garinsu kuma suna neman kudin fansa

Wasu mazauna garin Gauraka da ke karamar hukumar Tafa na jihar Niger, a ranar Litinin sun tare titin Abuja-Kaduna suna zanga-zanga kan yawan sace mutane da ake yi a garin,The Cable ta ruwaito.

Garin na Gauraka na kan babban hanyar Abuja zuwa Kaduna ne.

Masu zanga-zangar sun dakatar da zirga-zirgan motocci a kan titin yayin da suke kona tayoyi domin janyo hankulan mutane.

Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi
Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici

Mutanen garin na zanga-zangar ne domin sace wasu yan uwansu da yan bindiga suka yi.

Sun ce an sace kimanin mutum 30 daga garin kuma har yanzu suna hannun masu garkuwa inda suke neman kudi masu yawa kafin su sako su.

Masu zanga-zangar sun ce sun yi hakan ne domin janyo hankalin hukumomin da abin ya rataya a kansu bayan yan bindigan sun afka garin misalin karfe 1 na dare sun sace mutum 15.

Da ya ke magana yayin zanga-zangar, wani mazaunin garin mai suna Hassan Hassan ya ce yan bindigan sun afka garin misalin karfe 1.17 na dare sun sace mutum 15.

Ya ce sun yanke shawarar yin zanga-zangan ne domin neman gwamnati ta kawo musu dauki a jihar Niger.

KU KARANTA: Tambuwal Ya Ware Wa Malamai N155m Don Da'awar Addinin Musulunci

Wani mazaunin mai suna Dare ya ce a ranar Alhamis da ta gabata yan bindigan sun sace mutum hudu kuma suna neman Naira miliyan 10 kudin fansa.

Ya ce mutanen unguwar sun sanar da yan sanda amma an ce musu babu makamai da motocci da za a dakile harin.

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164