Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP
- Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya yi wa tsohon gwamnan Niger Babangida Aliyu wankin babban bargo
- Wike ya bayyana Aliyu a matsayin 'ɗan leken asiri' kuma babban matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
- Wike ya yi wannan jawabin ne sakamakon hirar da aka yi da Aliyu a wasu jaridu inda ya yi zargin cewa Wike na mulkin kama karya a PDP
Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito.
DUBA WANNAN: An Sallami Malaman Makarantun Frimare 20 Daga Aiki a Niger
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.
Amma Wike ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin tantirin maƙaryaci, yana mai cewa Aliyu ya taɓa cewa shi da wasu tsaffin gwamnonin arewa sun yi wa jam'iyyar PDP zagon ƙasa a zaben 2015.
Wike ya ce wasu gwamnonin daga arewa da suka hada da Jonah Jang na Plateau da Sule Lamiɗo na Jigawa sun tsame kansu daga wannan cin amana ta Aliyu.
Ya ce, "Babu shugaba mai mulkin kama karya a jam'iyyar PDP a jihar Rivers. Hakan yasa PDP ke da tabbacin lashe kowanne zaɓe da za a yi a kasar nan.
"Amma ba haka abin ya ke a Niger ba. Kun ga martanin da tsohon shugaban ƙasa ya yi masa. Kawai son tada zaune tsaye ya ke yi da cin amana."
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Kofar Gidanta
Ya ce Aliyu na daga cikin wadanda ba su so Uche Secondus ya zama shugaban PDP na ƙasa ba amma daga bisani ya zama tamkar kakakin kwamitin Ayyuka na Ƙasa na jam'iyyar ƙarƙashin jagorancinsa.
Wike ya kuma yi ikirarin cewa Aliyu bai da wani aiki na azo-a-gani da ya yi a Niger kuma baya iya kawo jiharsa a lokacin zaɓe.
Awani labarin daban, kunji wasu mazauna garin Gauraka da ke karamar hukumar Tafa na jihar Niger, a ranar Litinin sun tare titin Abuja-Kaduna suna zanga-zanga kan yawan sace mutane da ake yi a garin,The Cable ta ruwaito.
Garin na Gauraka na kan babban hanyar Abuja zuwa Kaduna ne.
Masu zanga-zangar sun dakatar da zirga-zirgan motocci a kan titin yayin da suke kona tayoyi domin janyo hankulan mutane.
Asali: Legit.ng