'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Kofar Gidanta

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Kofar Gidanta

- Yan bindiga sun sace matar mataimakin shugaba matasa na APC a jihar Oyo

- Masu garkuwar sun sace ta ne a kofar gidan ta a daren ranar Lahadi 23 ga watan Mayu

- Tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APC, Wasiu Sadare ya tabbatar da hakan

Yan bindiga sun sace matar shugaban matasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Oyo, Mrs Arikeade Oni-Salawu, a daren ranar Lahadi.

Independent ta ruwaito cewa an sace Mrs Salawu, likita, a gidan ta da ke Aromolaran, Old Ife Road, Ibadan.

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Oyo
'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Oyo. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi

Tsohon mai magana da yawun jam'iyyar, Wasiu Sadare, ya tabbatarwa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin a ranar Talata yana mai kira da jami'an tsaro su ceto ta.

Sadare ya ce, "Abin takaici ne. Ba mu son muyi magana domin mu ƙyalle jami'an tsaro su yi aikinsu.

"Muna fatan a sako ta da wuri. Har yanzu wadanda suka sace ta ba su tuntubi iyalan ta ba."

Majiyar Legit.ng ta gano cewa matan da aka sace tana tuki ne a motar mijinta, Mr Areokuta Salawu ta iso gida ta bude kofa sai suka yi awon gaba da ita.

KU KARANTA: Shugabannin Fulani Da Tibi Sun Amince Da Tsagaita Wuta a Taraba

"Da saukar ta domin bude kofar gida, masu garkuwar suka ɓullo dauke da muggan makamai da wasu abubuwa masu haɗari.

y"Sun sace matar. Misalin ƙarfe 10 na daren jiya," in ji shi.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sanda jihar, Adewale Osifeso ya ce zai yi bincike kafin ya yi bayan

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel