Jerin sunayen shugabannin jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas a cikin mako guda

Jerin sunayen shugabannin jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas a cikin mako guda

- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi babban kamu da mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas

- An tattaro cewa manyan jiga-jigan APC 11 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawar cikin mako guda a jihar

- Hakan ya kasance ne sakamakon rikicin cikin gida da APC ke fama da shi a reshenta na Ribas

Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar ya nuna cewa akalla jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) 11 a jihar Ribas sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a cikin makon da ya gabata.

Yakin neman daukaka tsakanin tsohon gwamnan jihar da ministan sufuri, Rotimi Amaechi da wasu shugabannin jam'iyyar APC ya tarwatsa jam'iyyar. Wannan ya ba shugabancin PDP dama don jan hankalin mambobin jam'iyyar adawa a jihar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe limamin Katolika, sun sace wani a Katsina

Jerin sunayen shugabannin jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas a cikin mako guda
Jerin sunayen shugabannin jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas a cikin mako guda Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa jaridar ta lura cewa wani tsohon shugaban jam'iyyar a jihar, Cif Davies Ikanya da wani tsohon dan majalisar dokoki ta kasa, Igo Aguma, tare da magoya bayan su za su kasance tare da jam'iyyar People Democratic Party (PDP) a hukumance kafin karshen ya kare.

Tambari Sydney Gbara, mai magana da yawun jam’iyyar, ya ce Gwamna, Nyesom Wike ne zai tarbi shugabannin biyu a wani biki da za a yi a Fatakwal a ranar Asabar, 22 ga Mayu.

Ga jerin sunayen sababbin shiga PDP a jihar Ribas a kasa:

1. Ikanya Davies (Shugaban Jam’iyyar APC na farko a Ribas)

2. Rt. Hon. Igo Aguma (Tsohon dan majalisar kasa kuma tsohon shugaban riko na APC)

3. Cif Ogbogbo Nnamdi (Tsohon shugaban karamar hukuma na APC)

4. Hon. Isobo Jack (Tsohon shugaban rikon kwarya, APC)

5. Cif Wisdom Wakama (Wizzy Waks)

6. (Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar jihar)

KU KARANTA KUMA: Matawalle Ya Bada Umurnin Rufe Kasuwanni Huɗu a Zamfara

7. Hon. Alpine Whyte (Tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Phalga)

8. Hon. Alamese Martins-Yellow

9. Hon. Ilamabo Mirilla

10. Hon. Faaye Franklin

11. Barr. Paul Nwankwoala (Tsohon mai ba da shawara kan harkokin shari'a na APC).

Ikanya, wanda ya kasance shugaban jam'iyyar APC na farko a jihar, ya jagoranci jam'iyyar tsakanin 2013 da 2018.

Sai dai APC reshen Ribas, ta dade tana fama da rikice-rikicen cikin gida wadanda ba a magance su ba wadanda suka hana jam'iyyar shiga zabukan 2019.

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa da gaske ta ke yi wajen ganin an gudanar da zabuka na gaskiya, kuma masu nagarta.

Mai girma Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya yarda kowane ‘dan kasa yana da damar da zai zabi duk wanda yake so a matsayin shugabansa.

Jaridar The Cable ta rahoto shugaban kasar yana cewa mutane sun saba yin ‘a mutu-ko-a yi rai’ domin ganin sun samu kujerar siyasa a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel