Jerin jiragen yaki masu karfi 26 da gwamnatin Buhari ta siya tun daga 2015

Jerin jiragen yaki masu karfi 26 da gwamnatin Buhari ta siya tun daga 2015

Daya daga cikin alkawuran yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015 shi ne inganta kayayyakin aiki na Sojojin Saman Najeriya (NAF) da sauran hukumomin tsaro.

A cewarsa, wannan matakin an yi shi ne domin yaki da ta'addanci, masu tayar da kayar baya, 'yan fashi da makami, da sauran barazanar tsaro a Najeriya.

Ya zuwa yanzu an cimma shawarar da gwamnatin Buhari ta yanke na samar da kayan aiki ga sojojin sama da na Sojojin Najeriya (AFN) don haɓaka ƙwarewar aiki da isar da shi.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen shugabannin jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas a cikin mako guda

Jerin jiragen yaki masu karfi 26 da gwamnatin Buhari ta siya tun daga 2015
Jerin jiragen yaki masu karfi 26 da gwamnatin Buhari ta siya tun daga 2015 Hoto: @hqnigerianairforce
Asali: Facebook

Shugaban na Najeriya ya isar da alkawarin da ya yi na karfafa karfin tsaro ta hanyar sayen jirage masu saukar ungulu da jiragen yaki.

Za a tura jirgin saman ne domin yaki da masu tayar da kayar baya a kasar.

Legit.ng a cikin wannan zauren ya lissafo sabbin jiragen sama na NAF 26:

1. Jirgin horarwa ta Super Mushshak guda 10

2. Jirage masu juyawa guda 13 da suka kunshi

A. Jiragen harbi masu saukar ungulu na Mi-35M guda 5

B. Jirage masu saukar ungulu na Agusta 109 Power guda 4

C. Mi-171E guda 2

D. Jirage masu saukar ungulu na Bell 412 guda 2

3. Jiragen sama na JF-17 Thunder guda 3

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe limamin Katolika, sun sace wani a Katsina

Wadanda ake tsammanin isowarsu daga baya sune:

1. Wasu karin guda 20 daga Amurka wadanda suka kunshi jiragen A-29 Super Tucano guda 12. Jiragen UAVs guda 8.

A wani labarin, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ranar Alhamis, ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku da gwamnatinsa ta siyo wa rundunar sojin sama (NAF), kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Shugaban ya miƙa jiragen ne a sansanin sojin dake Makurɗi yayin bikin cikar NAF shekaru 57 da kafuwa, kamar yadda guardian ta ruwaito.

Shugaba Buhari, wanda ministan tsaro, Bashir Magashi, ya wakilta yace jiragen yaƙin JF-17 da aka ƙara zuwa kayan aikin NAF zasu taimaka sosai wajen yaƙin da rundunar take yi da yan ta'adda, yan bindiga da sauran manyan laifuka da ƙasar ke fama dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel