Ma’aikatar Noma Ta Ce Ta Gina Wa Makiyaya Masallaci Na N30m a Borno

Ma’aikatar Noma Ta Ce Ta Gina Wa Makiyaya Masallaci Na N30m a Borno

- Ma'aikatar Noma ta tabbatar da wasu bayanai da suke kunshe cikin wata takarda da ta fito daga ma'aikatar

- Ma'aiktar Noman ta ce gaskiya ne cewa ta ware miliyoyin naira domin yi wa makiyaya da Boko Haram suka kora daga gidajensu gine-gine

- Sanarwar da direktan watsa labarai na hukumar ya fitar ta ce an bi dukkan dokoki da tsare-tsare da suka dace kafin yin ayyukan

Ma'aikatar Noma da Raya Karkara, a ranar Alhamis ta tabbatar da abin da wani takardar gwamnati ya kunsa tana mai cewa takardar sahihi ne kuma ta gina wa makiyaya masallaci ne, The Punch ta ruwaito.

Ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da Direktan Watsa Labarai na Ma'aikatar Noma, Theodore Ogaziechi ya fitar yana mai cewa yan ta'addan Boko Haram ne suka koro makiyayan daga muhallinsu a Borno.

Ma’aikatar Noma Ta Ce Ta Gina Wa Makiyaya Masallaci Na N30m a Borno
Ma’aikatar Noma Ta Ce Ta Gina Wa Makiyaya Masallaci Na N30m a Borno. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa

Ta ce, "Domin fayyace gaskiya, takardar da aka fitar sahihi ne kuma ba a kan tsari ya ke.

"Ba na bogi bane kuma ma'aikatar ne ta fitar da shi domin gina wurin bauta domin wasu makiyaya da Boko Haram ta raba su da muhallansu kuma aka sake musu wuri a kananan hukumomin Ngarannam/Mafa a jihar Borno."

Ma'aikatar ta ce baya ga masallacin, an samar musu wasu kayayyaki da suka hada da famfao mai amfani da na'urar samar da lantarki ta hanyar amfani da hasken rana da tankuna da wuraren da dabobinsu za su yi kiwo.

Saura sun hada da kayan girbe amfanin gona, cibiyar tatsar madarar shanu, gidajen zama da gine-gine da makiyayan za su zauna.

KU KARANTA: Bayan Komawa APC, Ayade Ya Aike Da Muhimmin Saƙo Ga Tsaffin Takwarorinsa a PDP

"Ginin masallacin wata bukata ce ta musamman da mutanen suka nema ta hannun gwamnatin jihar Borno domin kada su rika zuwa wuri mai nisa domin yin sallah da kuma tabbatar da cewa ba su hadu da yan ta'adda ba," a cewar ma'aikatar noman.

Bugu da kari, ma'aikatar ta ce kowa na iya samun takardar domin ya duba sannan bata shakkar wani abu domin ta samu amincewa da ya dace kafin gudanar da ayyukan kuma an bi doka.

A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.

An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel