2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa

2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa

- Wani matashi dan shekara 35, Aminu Sa'idu mai neman takarar shugaban kasa ya ziyarci Ahmed Musa

- Aminu Sa'idu ya ce ya ziyarci kyaftin din na Kano Pillars ne domin neman shawara da tallafi

- Ahmed Musa, a bangarensa ya ce bayyana ziyarar a matsayin matakin da ya dace kuma a lokacin da ya dace

Aminu Saidu, wani bakano dan shekara 35 da ke neman takarar shugaban kasa, a ranar Alhamis, ya bayyana niyarsa na neman takarar neman kujerar shugaban kasar Nigeria sannan ya nemi taimakon fitaccen dan wasan kwallon kafa Ahmad Musa, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar matashin mai neman takarar, gabanin babban zaben shekarar 2023, ya ce ya yanke shawarar fara neman tallafi ne daga kowanne sashi da ke taka muhimmin rawa wurin cigaban kasa.

2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa
2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa. Hoto:@daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bayan Komawa APC, Ayade Ya Aike Da Muhimmin Saƙo Ga Tsaffin Takwarorinsa a PDP

Ya ce matasan Nigeria sun kasance suna taka muhimmiyar rawa wurin kawo cigaba a bangarori daban-daban don haka akwai bukatar a farkar da su su fahimci kallubalen da ke gabansu.

"A matsayina na matashi dan Nigeria da ke fatan zama shugaban kasa a 2023; yana da muhimmanci in fara tuntubar matasa na gida da waje kamar irinsu Ahmed Musa don neman shawara da tallafi," in ji shi.

Matashin mai neman takarar ya kara da cewa matasan Nigeria na da muhimmin rawa da za su taka wurin tabbatar da cewa Nigeria ta cigaba a kowanne bangare.

A bangarensa, Ahmed Musa ya ce ziyarar da matashin dan takarar Aminu Sa'idu ya kai masa a matsayin mataki mai kyau a kuma lokacin da ya dace.

KU KARANTA: Allah Ya Yi Wa Sarkin Funakaye Muhammadu Kwairanga Abubakar II Rasuwa

Idan za a iya tunawa, Aminu ya bayyana niyarsa na takarar shugabancin kasa tun farkon wannan shekarar yana mai alwashin amfani da damar dokar 'not too young to run' da aka yi wacce ta rage shekarun masu shiga takara.

A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.

An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel