Eidul Fitr: Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Faɗin Najeriya

Eidul Fitr: Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Faɗin Najeriya

- Muƙaddashin Sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Baba, ya umarci a ƙara tsaurara tsaro a faɗin ƙasar nan

- Sufetan ya bayyana haka ne a wani jawabi da rundunar yan sanda ta fitar

- Hukumar yan sanda ta taya musulmin duniya murnar zagayowar sallah ƙarama (Eidul Fitr) bayan kamma azumin Ramadan

Yayin da mabiya addinin musulunci ke shagalin zagayowar ƙaramar sallah (Eidul Fitr), muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Baba, ya bada umarnin tsaurara tsaro.

KARANTA ANAN: Mun San Inda Masu Satar Mutane Suke, Muna Tsoron Matsala ne Kawai, Lai Muhammed

Baba ya kuma amince da tura wasu jami'an yan sanda zuwa wasu sassan ƙasar nan tare da kayan aiki domin ƙara ƙarfafa tsaro har zuwa bayan shagalin sallah, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Sufetan ya bayyana cewa wannan umarnin wani ɓangarene na ƙoƙarin da hukumar yan sanda ke yi na inganta zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.

Eidul Fitr: Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Faɗin Najeriya
Eidul Fitr: Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Faɗin Najeriya Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Ya kuma tabbatarwa yan Najeriya cewa hukumar yan sanda ƙarƙashin sabon tsarin da yazo dashi, zata inganta tsaro da kuma gano hanyoyin dakile ayyukan ta'addanci da Najeriya ke fama dasu.

KARANTA ANAN: Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa

Jawabin da hukumar yan sanda ta fitar, yace:

"Sufetan yan sanda ya umarci kwamishinonin yan sanda dake jihohin ƙasar nan tare da Birnin tarayya, Abuja, cewa su tabbatar da inganta tsaro, hakanan ya gargaɗi jami'an da aka tura domin gudanar da wannan aikin da su nuna ƙwarewa a aikinsu."

"A madadin muƙaddashin sufetan yan sanda tare da jami'ansa na miƙa saƙon taya murna ga mabiya addinin musulci na Najeriya da na duniya baki ɗaya bisa zagayowar Eidul Fitr."

"Hukumar yan sanda na roƙon su da su yi amfani da darussan da suka koya a watan Ramadan a ayyukansu na yau da kullum."

A wani labarin kuma Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS

Tsohon shugaban hukumar Inshoran lafiya NHIS, Usman Yusuf, yace yan bindiga na buƙatar tattaunawar zaman lafiya da malamai.

Yusuf yace ya fahimci haka ne a taron da ya halarta da yan bindiga kala-kala a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel