Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS

Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS

- Tsohon shugaban hukumar Inshoran lafiya NHIS, Usman Yusuf, yace yan bindiga na buƙatar tattaunawar zaman lafiya da malamai

- Yusuf yace ya fahimci haka ne a taron da ya halarta da yan bindiga kala-kala a ƙasar nan

- Yace ba yanda za'ai a magance wannan matsalar ta tsaro da ƙarfi kaɗai, domin mutanen nason su bar wannan ɗanyen aikin da suke yi

Tsohon shugaban hukumar inshoran lafiya ta ƙasa (NHIS), Usman Yusuf, yace yan bindiga na buƙatar tattaunawar zaman lafiya da malamai.

KARANTA ANAN: Rundunar Soji Ta Bayyana Matakin da Zata Ɗauka Kan Zargin da Ake Mata a Jihar Zamfara

Yusuf ya bayyana cewa ya fahimci haka ne a taron da suka yi da yan bindigan kala daban-daban.

Yayin da yake jawabi a wata tattaunawa da yayi da gidan talabishin na Arise Tv ranar Talata, Yusuf yace:

"Wannan shine abinda muka gano a dukkan jihohi biyar da muka je, yan bindigan suna son sauraron malamai. A jihar Neja sun tattaro kwamandoji daga jihohi biyar, kuma sun saurari malaman da muka je dasu."

"Da alama su kansu sun gaji da wannan mummunan aikin da suke aikatawa, suna buƙatar tattaunawa da malamai domin kawo zaman lafiya mai ɗorewa."

Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS
Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yusuf ya kara da cewa duk da akwai rawan da jami'an tsaro ke takawa wajen dawo da zaman lafiya, hakan ba zai hana a zauna dasu domin sulhu ba.

KARANTA ANAN: Kungiyar Inyamurai Ta Ɗau Zafi Bisa Zargin Jami’an Soji Na Shirya Mata Wata Maƙarkashiya

Yace: "Akwai rawar da jami'an tsaro ke takawa sosai, domin idan da babu jami'an tsaro da yanzun Boko Haram ta ƙwace yankin arewa maso gabas ya koma ƙarƙashinsu."

"Hakanan da yanzun yan bindiga sun kwace arewa ta tsakiya, saboda haka akwai rawar da jami'an tsaro ke takawa, amma duk wanda yace maka za'a warware wannan matsalar da ƙarfi to tabbas bai san abin yake ba.

"Bazai yuwu a warware wannan matsalolin da karfi ba, bai kamata mu cigaba da saka bam ga mutanen da yakamata ace mun gyara rayuwarsu ba."

A wani labarin kuma Ba Za’a Ga Watan Sallah Ba Sai Ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA

Hukumar binciken sararin sama ta ƙasa NASRDA tayi hasashen cewa jinjirin watan shawwal ba zai bayyana ba sai ranar Laraba 12 ga watan Mayu.

Hukumar tace idan har hasashen ta ya zama gaskiya, musulmai zasu gudanar da sallar Eid Fitr a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel