Talauci Ke Ƙara Rura Wutar Ta’addanci a Nigeria, Shehu Sani

Talauci Ke Ƙara Rura Wutar Ta’addanci a Nigeria, Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya alakanta talauci da karyewar tattalin arziki da ta'addanci a arewacin Nigeria

- Shehu Sani ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke martani kan hare-haren da ake kai wa Arewa maso Gabashin Nigeria

- Sanata Sani ya bayyana damuwarsa kan rahoton cewa yan ta'adda na raba wa mutane N20,000 a gidajensu a jihohin Borno da Yobe

Tsohon sanatan Kaduna mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya ce talauci da wahalhalun da talakawa ke ciki ne ke kara rura wutar rashin tsaro musamman a Arewa maso Gabas.

Shehu Sani ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke martani kan hare-haren da yan ta'adda ke kaiwa a Arewa maso Gabas da wasu sassan kasar.

DUBA WANNAN: Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun

Talauci Ke Ƙara Rura Wutar Ta’addanci a Nigeria, Shehu Sani
Talauci Ke Ƙara Rura Wutar Ta’addanci a Nigeria, Shehu Sani. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

Da ya ke kokawa kan matsalolin a Twitter a ranar Talata, tsohon dan majalisar ya bayyana damuwarsa game da sabon tsarin da yan ta'addan Boko Haram da ISWAP ke yi na raba wa mutanen da suke kaiwa hari kudade a Yobe da Adamawa.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

"A watan da ta gabata, Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun rabawa mutanen garin da suka kai wa hari N20,000; Yanzu kuma yan ta'addan ISWAP na rabon kayan abinci a wasu garuruwa a jihohin Yobe da Borno; Darasin a nan shine akwai mummunan talauci da ke rura wutar ta'addanci a Arewa maso Gabashin kasar mu.

"Idan yan ta'adda sun kashe talakawa, yan ta'addan miyagu ne; Idan yan ta'adda sun ciyar da talakawa, gwamnati ce muguwa," kamar yadda Shehu Sani ya kara rubutawa a Twitter.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel