Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun

Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun

- Gwamnatin jihar Osun ta bada umurnin rufe babban masallacin Inisa a karamar hukumar Odo-Otin

- Hakan ya biyo bayan rikicin limanci da ake yi ne tsakanin mutanen garin wadda ya yi sanadin rasuwar limamai biyu

- Gwamna Oyetola ya tura jami'an tsaro zuwa garin domin tabbatar da bin dokar da ya ce ba za a janye ba sai an warware matsalar nan gaba

Gwamnatin jihar Osun ta rufe babban masallacin Inisa da ke karamar hukumar Odo-Otin da ke jihar bayan limamai biyu sun mutu kan rikicin limanci a masallacin, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin jihar ta kuma haramta yin sallar jami'i a babban masallacin da filin sallar idi na garin.

Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun
Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu

A sanarwar da aka fitar mai dauke da sa hannun mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar, Prince Abdullah Adeyanju Binuyo, gwamnatin jihar ta ce masallacin zai cigaba da kasancewa a rufe har sai baba-ta-gani.

Binuyo ya ce matakin da gwamnatin ta dauka ya zama dole ne duba da cewa mutanen musulmi na garuruwan biyu sun gaza cimma matsaya don nada limamin masallacin.

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

A cewar sanarwar, "a wani mataki na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin mutanen yankin da jihar, Gwamna Adeboyega Oyetola ya umurci a rufe babban masallacin garin domin kare afkuwar rikicin addini ko tsakanin mutanen yankuna.

"An tura jami'an tsaro zuwa garin domin su tabbatar an rufe masallacin kuma ba a yi sallar Idi a filin Idin ba.

"Wannan umurnin zai cigaba da aiki har zuwa lokacin da aka warware matsalar cikin maslaha."

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel