Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

- 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai hari wasu unguwanni a Maiduguri sun kona gidajen mutane

- Wani mazaunin Maiduguri da ya yi magana ta wayar tarho ya ce mutane suna ta tserewa daga gidajensu

- Amma daga bisani dakarun sojojin Nigeria sun fatattake yan ta'addan duk da cewa ba a tabattar da irin barnar da suka yi ba

Mayakan kungiyar Boko Haram sun cinna wuta a wasu a gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Ana kuma jin karar harbin bindiga da abubuwa masu fashewa a sassan birnin daban-daban musamman kusa da Jiddari Polo.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Dawo da Dokar Kulle da Hana Taron Mutane Soboda Korona

Yanzu-Yanzu: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri
Yanzu-Yanzu: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri
Asali: Original

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa ana musayar wuta tsakanin sojoji da wasu da ake zargin yan ta'adda ne a kusa da Molai da Jiddari a babban birnin jihar.

"An ji a kalla karar abin fashewa uku a Maiduguri. Ana harbe-harben bindiga a halin yanzu, farar hula suna tserewa daga gidajensu suna tafiya hanyar Damboa da tsohuwar GRA," a cewar majiyar tsaro.

KU KARANTA: Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu

Wani mazaunin garin da ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce bashi da wurin zuwa a halin yanzu saboda halin da ake ciki.

"A yanzu babu inda zan iya tafiya. Ba zan iya zuwa gida ba. Kana iya jin karar harbin bindigan?" in ji shi.

'Yan ta'addan sun kai harin ne a daidai lokacin da musulmi ke shirin yin bude baki a cikin watan Ramadan mai albarka.

Daga bisani, zaratan dakarun sojoji sun fatattake yan ta'addan amma a halin yanzu ba a kiyasta adadin barnar da yan ta'addan suka yi ba.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel