Wata Sabuwar Cuta Da Ta 'Bulla Ta Kashe Mutane 6 a Kano

Wata Sabuwar Cuta Da Ta 'Bulla Ta Kashe Mutane 6 a Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar ta ce wata bakuwar cuta da ta bulla a jihar ta yi sanadin rasuwar mutane shida

- Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa ne ya tabbatar da hakan a ranar 7 ga watan Mayu

- Ibrahim-Tsanyawa ya ce ma'aikatar lafiya tana bincike a kan cutar da nufin gano matsalar yayin da ake jinyar sauran wadanda suka kamu

Gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Wata Sabuwar Cuta Da Ta 'Bulla Ta Kashe Mutane 6 a Kano
Wata Sabuwar Cuta Da Ta 'Bulla Ta Kashe Mutane 6 a Kano. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Kama Hatsabibin Ɗan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mutane Fyaɗe a Sokoto

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

"Ana danganta bullar cutar da yin bayan gida a fili da rashin tsaftace muhalli a garuruwan.

"Wadanda cutar ta kamu da su suna amai da gudawa.

"Cutar ta kashe mutane shida, an sallami 28 daga asibiti yayin da sauran 18 suna nan suna jinya a asibitin," in ji shi.

KU KARANTA: Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa

Ibrahim-Tsanyawa ya ce ma'aikatar lafiya na jihar ta fara bincike domin gano abin da ya yi sanadin wannan cutar mai daure kai.

A yayin da ya ke jadada kokarin gwamnatin jihar wurin cigaba da wayar da kan mutane da kiyayewa, Ibrahim-Tsanyawa ya bukaci mutanen garin su rika tsaftace muhallinsu da jikinsu don takaita yaduwar cutar.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel