Labari Da Ɗumi-Ɗumi: Afenifere Ta Buƙaci Buhari Ya Yi Murabus

Labari Da Ɗumi-Ɗumi: Afenifere Ta Buƙaci Buhari Ya Yi Murabus

- Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus

- Kungiyar ta bakin mukadashin shugabanta, Ayo Adebanjo ta ce Buhari ya gaza magance matsalar tsaro da tattalin arziki

- Cif Adebanjo ya ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa Buhari ya yi murabus idan yana son tsira da mutuncinsa

Kungiyar kare hakkin yarabawa ta Afenifere, a ranar Talata, ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda gazawar gwamnatinsa wurin magance matsalar tsaro da talauci a kasar.

Kungiyar ta ce yanzu ne lokaci da ya fi dacewa shugaban kasa ya yi murabus domin kiyaye mutuncinsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Labari Da Ɗumi-Ɗumi: Afenifere Ta Buƙaci Buhari Ya Yi Murabus
Labari Da Ɗumi-Ɗumi: Afenifere Ta Buƙaci Buhari Ya Yi Murabus. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

Mukadashin shugaban kungiyar na kasa, Cif Ayo Adebanjo ya ce gwamnatin Buhari ta gurgunta kasa kuma ta gaza magance matsalar tsaro da tattalin arziki.

Ya yi wannan furucin ne a wurin taron bikin cika shekaru 95 na shugabansu da karrama Cif Reuben Fasoranti a karamar hukumar Akure ta Arewa

Ya ce Shugaban kasar ya bawa yan Nigeria kunya kuma yanzu ne lokacin da ya fi dacewa ya bar gwamnati, yana mai cewa gwamnatin Buhari ba za ta iya magance matsalolin ba.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Dawo da Dokar Kulle da Hana Taron Mutane Soboda Korona

Adebanjo ya ce: "Na fada musu cewa a kasashe na gari da suka cigaba, da tuni ya sauka daga kujerarsa.

"Idan ta yana mutunta kansa, da ya tafi gomin ya gaza.

"Mene ya ke shugabanta? Rashawa ne? tsaro, ilimi?

"Babu doka da oda a kasar tsawon shekaru uku da suka shude.

"Kawai saboda 'yan Nigeria sun fiye hakuri da shugabanni masu kama karya ne shi yasa har yanzu bai sauka ba."

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel