Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Dawo da Dokar Kulle da Hana Taron Mutane Soboda Korona

Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Dawo da Dokar Kulle da Hana Taron Mutane Soboda Korona

- Gwamnatin tarayyar Nigeria ta sake dawo da dokokin takaita fita a jihohi 36 da Abuja saboda korona

- Dokar ta haramta wa mutane fita daga karfe 12 na dare zuwa 4 na asubahi a dukkan jihohin kasar

- Har wa yau, an sake kafa dokar hana taron mutane fiye da 50 sannan an bada umurnin rufe wuraren taron mutane kamar klub, mashaya da wurin motasa jiki (gym)

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta sake dawo da dokar takaita fita a dukkan kasar daga 12 na dare zuwa 4 na asuba domin dakile yaduwar annobar korona wato COVID-19, The Nation ta ruwaito.

Mukhtar Mohammed, manaja kula da yaduwar cuta na kasa ne ya sanar da hakan yayin jawabin da kwamitin shugaban kasa kan korona ta yi a Abuja.

Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Saka Dokar Hana Taron Jama’a Saboda Korona
Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Saka Dokar Hana Taron Jama’a Saboda Korona. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A Tsige Buhari Idan Bai Zai Iya Samar Da Tsaro Ba, Hakeem Baba-Ahmad

Mohammed ya ce dokar takaita fitar za ta fara iki daga daren ranar Litinin.

Ya kuma ce daga ranar Talata za a rufe wuraren casu na dare, wuraren motsa jiki wato gym da sauran wuraren cinkoson mutane har zuwa wani lokaci nan gaba.

Ya ce an bada umurnin rage adadin mutanen da ke hallartar wuraren ibadah da kashi 50 cikin 100 yayin da za a cigaba da yin sauran taro da harkoki na gwamnati ta hanyar amfani da fasahar bidiyo na intanet.

Ya ce za a takaita duk wani taron mutane zuwa mutum 50 a kowane lokaci.

Ba za a bari mutane su shiga hukumomin gwamnati ba har sai suka saka takunkumin fuska.

KU KARANTA: An Kama Hatsabibin Ɗan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mutane Fyaɗe a Sokoto

Ya kara da cewa masu tafiya kasashen waje domin yin ayyuka masu muhimmanci suna iya yin hakan amma dole su bi dukkan dokokin dakile yaduwar cutar.

Kazalika, ya ce ba a takaita tafiye-tafiye a tsakanin jihohin Nigeria ba.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel