An Yi Zanga-Zanga a BUK Kan Kashe Wani Ɗalibi a Jami'ar

An Yi Zanga-Zanga a BUK Kan Kashe Wani Ɗalibi a Jami'ar

- Daliban jami'ar BUK na zanga zangar kashe abokin su amma jami'ar ta ce wanda aka kashe ba dalibinta bane

- Hukumar makarantar ta ce ba dalibinta bane ziyara ya kawo kuma ba a cikin makarantar lamarin ya faru

- Daliban da suke zanga zangar sun bukaci a samar da tsaro a makarantar biyo bayan faruwar lamarin

Daliban jami'ar Bayero da ke Kano, ranar Litinin sunyi zanga zanga kan kashe wani dalibi dan uwan su dalibi a sabon sashen jami'ar (new site), The Punch ta ruwaito.

Amma mai magana da yawun jami'ar, Lamara Garba, a wata sanarwa da ya fitar dangane da batun, ya ce wanda aka kashe ba dalibi bane ziyara ya je.

An Yi Zanga-Zanga a BUK Kan Kashe Wani Ɗalibi a Jami'ar
An Yi Zanga-Zanga a BUK Kan Kashe Wani Ɗalibi a Jami'ar. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Dawo da Dokar Kulle da Hana Taron Mutane Soboda Korona

Daliban jami'ar sun shiga zanga-zangar ne bayan sun samu labarin mutuwar dalibin a kafafen sada zumunta.

An gudanar da zanga-zangar a cikin makaranta dauke da takardu da maganganu daban-daban kamar 'an kasa tsare mata', 'sai wanda ke da rai ne zai zana carryover' 'kuyi aiki da hankalinku', 'muna bukatar tsaro a BUK, duka cikin harshen turanci, da sauran maganganu da dama.

Daliban da suke zanga-zangar sun bukaci hukumar jami'ar da ta tsare dalibai bayan yawaitar rashin tsaro a makarantar.

Sai dai, da aka tuntube shi, mai magana da yawun jami'ar, Malam Garba, ya ce wanda aka kashe ba dalibin jami'ar bane ziyara ya kawo.

KU KARANTA: Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu

A cewar sa, wanda aka kashe shine Adamu Sunusi Shanono.

Garba ya ce masu kwacen waya ne suka kashe shi, ya kara da cewa an kama mutum biyu da ake zargi akan lamarin.

"Da wanda aka kashe da wanda ake zargin duka ba daliban makarantar bane kuma ba a cikin makarantar abin ya faru ba," in ji Garba.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel