Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu

Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu

- Wata doka a kasar Afirka ta Kudu na gab da amincewa mata auren mace fiye da daya

- Dokar wadda zata yi watsi da tsarin ko wanne addinai, an fara jin ra'yoyin mutane akai

- Akwai zabi guda uku a cikin takardar jin ra'ayoyin don samar da daidaito a dokar

Kamar yadda aka yarda da auren mace fiye da daya a wasu kasashen, wata sabuwar dokar aure a Afirka ta Kudu na iya bawa mace damar auren fiye da miji daya kwanan nan.

Dokar na daya daga cikin wadda aka fi nuna bukata a wata takardar jin ra'ayoyin mutane akan dokar aure.

Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu
Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

An fitar da kundin dokoki mai shafuka 67 wanda sashen kula da al'amuran zamantakewa ya fitar a satin nan.

DUBA WANNAN: Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa

Sashen a cikin kundin ya karfafa cewa ana so a kirkiri sabuwar dokar aure a kasar don rushe na halattattun aure da aka sani

Dokar auren Hindu, Yahudawa, Musulmi da Rastafariya duk basa cikin dokokin Afirka ta Kudu, a daya bangaren kuma ana ganin cewa dokar auren ba za ta samar da daidaito ba. An kara wannan cikin takardar neman jin ra'ayin.

"Rashin sanya auren wadannan addinai bai dace ba kuma ba abin aminta bane," a cewar kundin.

Takardar jin ra'ayin ta samar da nau'ikan aure uku don samar da daidaito a dokokin aure.

Doka ta farko ta bada damar auren gargajiya da na addinai, wanda zai bada damar gudanar da shagulgula ba tare da la'akari da banbancin launin fata ko kabila ko addinai ba.

KU KARANTA: An Kama Hatsabibin Ɗan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mutane Fyaɗe a Sokoto

Zabi na biyu zai bada damar aure irin na addini wanda ba zai shafi al'ada ba.

Zabi na uku zai zama wanda zai bada damar auren mace fiye da daya ga namiji ko namiji fiye da daya ga mace, a cewar kundin.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel