Gwamnatin Buhari na musgunawa kafafen watsa labarai, Atiku

Gwamnatin Buhari na musgunawa kafafen watsa labarai, Atiku

- Mr Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce gwamnatin Buhari tana take hakkin yan jarida

- Jigon na jam'iyyar PDP ya kuma ce gwamnatin na Buhari tana yi wa yan kasa barazana idan suna bayyana ra'ayoyinsu

- Atiku ya yi wannan furucin ne a rubutun da ya wallafa domin bikin ranar yan jarida na duniya na shekarar 2021

Tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Gwamnatin Buhari na musgunawa kafafen watsa labarai, Atiku
Gwamnatin Buhari na musgunawa kafafen watsa labarai, Atiku. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Atiku ya rubuta, "Bikin ranar Yancin Yan Jarida na duniya na nufin cewa kafafen watsa labarai na da yanci kuma mutane na da ikon fadin albarkacin bakinsu, kamar yadda ya ke cikin hakkin bil adama.

KU KARANTA: Korar Ma’aikata 30,000 da El-Rufai Ya Yi Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Kaduna, Ƙungiyar Ƙwadago

"Wadannan abubuwan biyu suna da muhimmanci a demokradiyya da ke aiki. Duk demokradiyyar da yan jarida ba su da yanci tamkar inji ne mara makamashi."

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel