An Kama Hatsabibin Ɗan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mutane Fyaɗe a Sokoto

An Kama Hatsabibin Ɗan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mutane Fyaɗe a Sokoto

- Jami'an NSCDC a jihar Sokoto sun kama wani hatsabibin mai fyade mai shekara 30

- NSCDC ta ce ta kama shi bayan samun rahoton wasu na dukkansa a Mabera ana shirin halaka shi

- Wanda ake zargin ya amsa cewa ya aikata laifin yana mai cewa shedan ne ya rinjaye shi

Jami'an hukumar tsaro ta Civil Defence reshen jihar Sokoto ta ce ta kama wani da ake zargi ya kware wurin fyade da cin zarafin yara a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito cewa Hamza Yusuf, dan shekara 30 da ake zargin ya ci zarafin yara 10 amma uku cikinsu kadai aka gano kawo yanzu.

An Kama Hatsabibin Dan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mata Fyade a Sokoto
An Kama Hatsabibin Dan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mata Fyade a Sokoto. Hoto: @daily_trust

KU KARANTA: Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa

A yayin jawabin da ya yi wa manema labarai, kwamandan NSCDC na jihar, Umar Musa Bala ya ce dukkan wadanda abin ya shafa ba su kai shekara 10 ba.

Ya ce an ceto wanda ake zargin ne a daidai lokacin da fusatattun mutane suka shirin halaka shi.

"An kira mu an sanar da mu cewa an kama wani da ake zargin mai fyade ne kuma za a halaka shi a Mabera, nan take muka bazama muka tafi.

"Mun ceto shi daga hannun wadanda ke shirin halaka shi muka kawo shi ofishin mu.

"Mun iya gano uku cikin wadanda ya ci zarafinsu kuma likitoci sun tabbatar da hakan sannan dukkansu shekarunsu bai kai 10 ba," in ji shi.

Bala ya kara da cewa za a bada belin wanda ake zargin saboda yajin aikin da ma'aikatan shari'a ke yi amma za a saka tsararan dokoki a belin.

DUBA WANNAN: El-Rufai Ya Sha Zafafan Martani Don Kalamansa Kan Ceto Ɗaliban Afaka

"Dole sai ya kawo wanda zai tsaya masa wanda zai zama sananne ne a garin kuma zai iya kawo shi a duk lokaci da ake bukata," in ji shi.

Ya kuma yi kira ga iyaye su rika sa ido a kan yaransu domin laifin ya zama ruwa dare.

Wanda ake zargin ya amsa cewa ya aikata laifin yana mai cewa shaidan ne ya rinjaye shi amma ya yi alkawarin ba zai sake ba.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel