Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa

Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa

- Wani mutum ya shiga wurin da ake casu ya bude wuta da bindiga ya kashe mutum shida a Colorado Springs, Amurka

- Bincike ya nuna cewa a cikin mutanen da mutumin ya bindige har da budurwarsa sannan daga bisani ya harbe kansa

- Rundunar ƴan sanda na Colorado Springs a ƙasar Amurka ta ce ta fara bincike don gano dalilin da ya janyo harbin

Wani mutum ya kusta wani wurin da ake casu da bindiga ya kashe mutum shida ciki har da budurwarsa kafin ya harbe kansa a Colorado, Amurka a cewar hukumomi, The Nation ta ruwaito.

Yan sanda sun isa wurin da abin ya faru sun tsinci gawar mutum shida da na bakwai da munanan rauni shima daga baya ya mutu a asibiti a ranar Lahadi a cewar sanarwar ƴan sandan.

Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa
Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: El-Rufai Ya Sha Zafafan Martani Don Kalamansa Kan Ceto Ɗaliban Afaka

Duk da ya ke akwai ƙananan yara a wurin casun da aka yi a ɗakin tafi da gidan ka, ba abin da ya same su.

"Wanda ake zargin, saurayin ɗaya daga cikin matan da suka hallarci casun ya shigo ɗakin ya fara harbi kafin daga bisani ya harbi kansa," a cewar sanarwar da ƴan sandan Colorado Springs ta fitar.

"Abokai, ƴan uwa da yara sun taru a ɗakin domin yin shagali ne a yayin da lamarin ya faru," a cewar sanarwar.

Kawo yanzu ba a gano dalilin da yasa mutumin ya aikata wannan lamarin mai muni ba.

Ƴan sanda sun rufe wurin da abin ya faru inda masu bincike suka hallara domin fara aikinsu.

Freddie Marquez, ɗan shekara 33, ya ce surukarsa na cikin wadanda abin ya rutsa da su yana mai cewa shima ya hallarci casun amma ya tafi misalin ƙarfe 10.30 na daren ranar Asabar.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Jarida, Sunyi Garkuwa da Matafiya da Dama a Katsina

Da tsakar dare yaron ɗaya daga cikin matan da suka hallarci casun ya kira shi a waya yana kuka.

"Wani ya shigo ya harbi kowa," Marquez ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters dangane da abin da aka faɗa masa a waya.

Gwamna Jared Polis ya ce harin ya faru ne a ranar Iyaye Mata na duniya a Amurka.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel