Da dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Sace Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar Katsina

Da dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Sace Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar Katsina

- Wasu 'yan bindiga sun afkawa masallaci a jihar Katsina, inda suka sace mutane sama da 40

- An ruwaito cewa, sun shigo ne cikin dare suka sace masallatan yayin da suke sallar Tahajjud

- Shaidu sun ce 'yan bindigan ba su yi harbi ba yayin harin har sai da suka gama sannan suka tsere

Akalla mutane 40 ne ‘yan bindiga suka sace a yayin da suke gudanar da sallar Tahajjud a wani masallaci da ke garin Jibiya na jihar Katsina.

Mazauna garin sun shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa ‘yan bindiga da dama sun kai hari a masallacin da misalin karfe 2 na daren Litinin kuma suka tafi da masu ibadar.

An tattaro cewa masu garkuwan da farko sun dauki mutane 47, ciki harda mata da yara, amma daga baya bakwai suka dawo.

"Ya zuwa yanzu mutane 40 ne suka bata bayan harin," in ji wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina Ta Tattara Mabarata Sama da 300 da Suka Tare a Filin Wata Makaranta

Da dumi-dumi: An yi Garkuwa da Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar Katsina
Da dumi-dumi: An yi Garkuwa da Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar Katsina Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wani mazaunin garin da ya bayyana haka, Lawal Jibiya, ya ce mazauna kauyukan sun sanar da su game da harin, bayan sun ga motsin 'yan bindigar da ke kan hanyar zuwa garin.

Ya ce daruruwan matasa da kungiyar 'yan banga da ke cikin garin suna cikin shirin ko ta kwana don tunkarar 'yan ta'addan, amma maharan suka sauya hanyarsu suka shiga garin daga mashigar yamma.

“Muna tsammanin su daga mashigar gabas ta hanyar Daddara, Kukar Babangida ko Magama amma a wannan karon sun wuce bayan gari suka yada zango a Jibawa.

"Daga Jibawa suka zagaya zuwa mashigar yamma kusa da asibitin Yunusa Dantauri kuma suka far wa wani masallaci a bayan gari," in ji shaidar.

A cewarsa, 'yan bindigan ba su yi harbi ko daya ba har sai da suka gama barnarsu.

Jibiya, wani gari ne da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Nijar, na daya daga cikin wuraren da ake yawan yin garkuwa da mutane da kuma yawaitar barnar ‘yan bindiga.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaha Mutane 11, Sun Jikkata 3 a Kauyen Katsina

A wani labarin, Gwamnatin Jihar Katsina a karshen mako ta kwashe mabarata sama da 300 daga wani yanki mallakar Kwalejin Horar da Malamai (ATC) da ke Katsina, Daily Trust ta rahoto.

Kwamishinan wasanni da jin dadin al'umma na jihar, Alhaji Sani Danlami, ya bayyana hakan yayin raba kayan tallafi ga mabaratan da abin ya shafa a tsohuwar gidan gwamnatin Katsina.

Yayin da yake jawabi ga mabaratan, Danlami ya ce gwamnatin jihar ba za ta sake amincewa da halayensu ba na mayar da makarantar gidajensu kamar ‘yan gudun hijira (IDPs).

Asali: Legit.ng

Online view pixel