Da Dumi-Dumi: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2020
- Hukumar jarrabawa ta NECO ta sanar da cewa, ta saki sakamakon jarrabawar shekarar 2020
- A yau Alhamis 6 ga watan Mayu ne shugaban hukumar ya sanar da fitar sakamakon a Minna
- Ya kuma bayyana kididdigan yadda sakamakon jarrabawar ta kasance, da kuma irin ci gaba da aka samu
Hukumar jarrabawar kammala sakandare a Najeriya ta NECO ta saki sakamakon jarrabawar shekarar 2020, jaridar Punch ta ruwaito.
Hukumar ta National Examination Council (NECO) ta sanar da hakan ne a birnin Minna na Jihar Neja a yau Alhamis 6 ga watan Mayun 2021.
Rajistira kuma shugaban hukumar, Godswill Obioma, ya ce dalibai akalla 41,459 ne suka yi rajistar rubuta jarrabawar, sai dai 39,503 kadai daga cikinsu ne suka rubuta ta.
KU KARANTA: An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Da Laifin Sayar Da Hodar Iblis
Ya ce an samu wadanda suka yi laifi guda 6,465 a 2020, ba kamar a 2019 ba inda aka samu 17,004.
Ya kara da cewa dalibai 26,277 sun samu kiredit biyar zuwa sama ciki har da yaren turanci (Inglishi) da lissafi, yayin da 34,014 suka samu kiredit biyar din ba tare da maudu'an guda biyu ba (Turanci da lissafi).
Shugaban wanda ya jaddada matsayar hukumar wajen kin amincewa da ayyukan rashin gaskiya, ya ce sun bi dukkan matakai da ka'idoji kafin sanar da sakamakon.
KU KARANTA: Iyayen Daliban Afaka Sun Ba Gumi Hakuri, Sun Ce Ba Shi Da Alaka Da Batun Fansar
A wani labarin, Farfesa Felicia Adebola Adedoyin, marubuciyar taken alkawarin kasa na Najeriya, ta mutu a ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.
Marigayiya Adedoyin wanda aka haifa a ranar 6 ga Nuwamba 1938 itace ta biyu cikin yara shida kuma Gimbiya daga Gidan Iji Ruling na Saki dake karamar hukumar Saki ta Yamma, yankin Oke Ogun na jihar Oyo.
Masaniyar a fannin ilimi, ta samu digirinta na uku a shekarar 1981 daga Jami’ar Legas, Nairaland ta rahoto.
Asali: Legit.ng