Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Ceto Mutane 13 a Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Kaduna

Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Ceto Mutane 13 a Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Kaduna

- Jaruman sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu mutane 13 daga hannun 'yan bindiga

- Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ceto mutanen ne a daren jiya Laraba 5 ga watan Mayu

- Sai dai, an ruwaito cewa, anyi asarar rayukan wasu 'yan kasa kafin a kubutar da mutanen 13

Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutum 13 daga hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar a daren jiya Laraba ba ta bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2020

Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Ceto Mutane 13 a Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Kaduna
Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Ceto Mutane 13 a Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Kaduna Hoto: thedefensepost.com
Asali: UGC

Mutanen a cewar Kwamishinan Tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, sun je Bakin Kasuwa da ke Karamar Hukumar Chikun domin yin aikatau a wata gona lokacin da 'yan bindigan suka kai musu harin.

Bayan samun bayanan sirri, sojojin sun bi diddigin 'yan bindigan cikin dajin da ke kusa da kauyen Bana, abin da ya kai ga ceto mutanen kenan.

A gefe guda kuma, 'yan bindigan sun kashe mutum biyu da aka bayyana da Ezekiel Iliya da Nasara Yohanna kafin zuwansu wurin, inda suka kona wata coci da kuma yashe kayayyaki daga wasu shaguna.

KU KARANTA: Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu

A wani labarin, Dalibai 27 na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, jihar Kaduna an sake su.

Daya daga cikin mutanen da suka karbi daliban ya tabbatar wa jaridar Daily Trust labarin. Ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Abubakar Gumi ne ya taimaka wajen sakin tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Daliban na daga cikin mutane 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel