Pantami: Shin za a rufe layin wadanda basu hada SIM dinsu da NIN ba?

Pantami: Shin za a rufe layin wadanda basu hada SIM dinsu da NIN ba?

- NCC ta fitar da wani sabon bayani dangane da alakanta NINs da katinan SIM

- A cewar hukumar, ba za a cire masu amfani da layin sadarwa gaba daya ba sakamakon rashin NIN

- Mai magana da yawun NCC, Ikechukwu Adinde, shi ma ya bayyana wasu fa'idodi da ke tattare da NINs da layukan waya kamar yadda gwamnati ta ba da umarni.

Legit ta ruwaito Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta ce ba za ta katse masu amfani da layin sadarwar ba sakamakon ci gaba da alakanta lambobin shedar kasa (NINs) da katinan SIM.

Daily Trust ta ruwaito cewa NCC a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 6 ga Janairu, ta ce bayanin ya zama dole don kawar da tsoron masu amfani da layuka da sauran jama’a.

An ruwaito mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Adinde yana cewa wani binciken da aka gudanar kwanan nan akwai kusan katinan SIM guda hudu zuwa biyar ga kowane dan Najeriya mai amfani da waya.

KU KARANTA: Tsarin zaben Amurka yafi na kasashen duniya ta uku muni -Trump

NIN: Shin za a rufe layin wadanda basu hada SIM dinsu da NIN ba?
NIN: Shin za a rufe layin wadanda basu hada SIM dinsu da NIN ba? Credit: NIMC
Source: Facebook

Ya ce wannan ya bayyana dalilin bayar da damar hada layukan SIM har guda bakwai zuwa NIN guda daya ta musamman a cikin wata sabuwar hanyar da gwamnatin Najeriya ta bude kwanan nan.

Adinde ya lura cewa idan akwai 'yan Najeriya miliyan 43 tare da NINs, wannan na iya samar da kimanin katin SIM miliyan 172 da tuni aka haɗa su da NINs.

Mai magana da yawun NCC ya bayyana cewa aikin da ake yi na hada NINs da katinan SIM domin amfanin dukkan yan Najeriya ne.

Legit.ng a baya ta ruwaito cewa NCC a baya ta baiwa kamfanonin sadarwar wa’adin mako biyu a watan Disamba na 2020 don cire katunan SIM da ba su da alaƙa da NINs.

Sai dai, bayan kukan da 'yan Najeriya suka yi, an ƙara wa'adin da mafi ƙarancin makonni uku.

A halin da ake ciki, Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa (NIMC) ta mayar da martani game da ikirarin cewa wadanda suka yi rajistar lambar tantancewa ta banki (BVN) suna da NIN kai tsaye.

KU KARANTA: Masu amfani da wutar lantarki sun ki amincewa da karin harajin wuta

A cewar kakakin NIMC, Kayode Adegoke, ikirarin ba daidai ba ne saboda dole ne hukumar ta fara tattara bayanan mutane kafin ta ware musu NIN.

Adegoke, ya yarda cewa hukumar a baya ta daidaita bayanan ta da wasu bayanan na BVN.

A wani labarin, Mataimakin mai kula da harkokin fasaha, na fasahar sadarwa a Ma’aikatar Sadarwa, Femi Adeluyi, ya yi bayani a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Alhamis, 31 ga Disamba, 2020, a Abuja.

Hukumar NIMC ta kirkiri wata manhajar wayar hannu da za a iya ganin bayanan katin dan kasa.

Ya ce ci gaban na daga cikin manufofin gwamnatin tarayya na inganta tsarin samun NIN da kuma danganta shi da layukan waya, da kuma daidaito da tsarin tattalin arzikin kasa na zamani na Najeriya, kamar yadda wakilin Legit ya ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel