Sai an lale mana N100m za mu fito da Shugaban karamar hukumar Kogi inji ‘Yan bindiga

Sai an lale mana N100m za mu fito da Shugaban karamar hukumar Kogi inji ‘Yan bindiga

- Miyagu sun dauke shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma a jihar Kogi

- ‘Yan bindiga sun sanar da cewa sai an bada N100m, Hon. Pius Kolawole, zai fito

- Shugaban kungiyar ALGON ya karbi tattaunawar da ake yi a madadin iyalinsa

Miyagun da su ka yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma a Kogi, sun yi maganar abin da za a biya domin kubutar da shi.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ‘yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar Honarabul Pius Kolawole.

Idan za ku tuna, an yi gaba da Pius Kolawole ne a kan iyakar Kogi da Kwara a karshen makon nan.

KU KARANTA: APC ta jefar da wasu masu sha’awar neman takarar kananan hukumomi a Kaduna

Wadannan ‘yan bindiga sun kira sakataren karamar hukumar Yagba ta yamma, su ka sanar da su game da kudin fansar da aka lafta a kan Hon. Kolawole.

Majiyar jaridar ta ce masu garkuwa da mutanen nan sun kuma tuntubi ‘yan uwan wannan Bawan Allah, su ka bukaci a aiko masu Naira miliyan 100.

‘Yan bindigan sun yi alkawarin za su sake tuntubar na-kusa da shugaban karamar hukumar a ranar Litinin domin cigaba da tattauna wa kan kudin fansar.

Jaridar ta ce an tsaida magana da masu garkuwa da mutanen za su sake tuntubar iyalinsa ta waya a jiya, amma har yamma ta yi, ba su iya kiran kowa ba.

KU KARANTA: Boko Haram sun hallaka Soja bayan sun sake kai munanen hari a Borno

Sai an lale mana N100m za mu fito da Shugaban karamar hukumar Kogi inji ‘Yan bindiga
Shugaban 'Yan Sandan Najeriya
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi, ALGON wanda shi ne shugaban karamar hukumar Ijumu, Taofik Isah, ya nemi a ceto abokin aikinsu.

Rahoton ya ce ‘yanuwan wannan Bawan Allah sun sallama wa Mista Taofik Isah da kungiyar ALGON su cigaba da tattauna wa da ‘yan bindigan a madadinsu.

‘Yanuwa da abokan arziki su na sa ran cewa ba da dade wa ba, za a kubutar da Pius Kolawole.

A jiya kun ji cewa Rundunar 'yan sanda reshen jihar Kogi ta tabbatar da kashe kwamishinan harkar fansho, Solomon Akeweje, sannan an sace Pius Kolawale.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP William Aya, ya tabbatar da hakan, ya ce kwamishinan da Kolawole su na cikin mota daya ne yayin da aka kai masu harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel