Mawaki ya rangadawa Ministan Buhari wakar batanci saboda ya fito ya tona masa asiri

Mawaki ya rangadawa Ministan Buhari wakar batanci saboda ya fito ya tona masa asiri

- Eidrez Abdulkarim ya yi waka, ya caccaki Ministan kwadago, Festus Kayemo

- Mawakin ya yi wannan wakar bayan Ministan ya fallasa alfarmar da ya nema

- Mai wakar ‘Najeriya jaga-jaga’ ya tabo Isa Pantami a wannan wakar da ya yi

Eedris Abdulkareem ya sake rera wata waka inda yake maida martani ga karamin Ministan kwadago da samar da ayyuka na tarayya, Festus Keyamo.

A ranar Litinin, jaridar Punch ta rahoto cewa mawakin ya sake koma wa shago, ya fito da wata sabuwar waka, ya na yi wa Festus Keyamo (SAN) raddi.

Jaridar ta ce mawakin ya rangada wannan waka ne bayan takkadamarsa da Festus Keyamo, wanda ya fallasa abin da ya faru tsakaninsu biyun a baya.

KU KARANTA: Keyamo: An soma biyan wasu cikin mutane 774, 000 da mu ka dauka aiki

A wannan sabuwar waka, Eidres Abdulkareem ya fito ya na cewa sun yi tunanin Festus Keyamo zai gyara abubuwa a kasa da ya samu kujerar Minista a 2018.

Mai wakar ‘Jaga-Jaga’ ya ce ya yi nadamar zaben Muhammadu Buhari. Har ila yau ya zargi gwamnatin nan ta gaza wa kan tsaro, ya ce ana kashe jama'a.

“A dalilin haka ne, na dauko maka wasikar da Obasanjo ya rubuta wa Buhari. Eh mutanenmu da yawa sun goyi bayan Buhari, amma duk mun yi da-na-sani.”

“Keyamo, gwamnatinku cike ta ke da furofaganda. Yanzu babu zaman lafiya a Najeriya. Ana garkuwa da yaranmu a makarantunsu.” Inji Eidres a wakar ta sa.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun cafke Eidres AbdulKareem da laifin doke Maigidansa

Mawaki ya rangadawa Ministan Buhari wakar batanci saboda ya fito ya tona masa asiri
Festus Keyamo da Eedris Abdulkareem
Asali: Instagram

“Jini na kwarara a birane da kauyuka. Zafin kishin addini ya zama tambarin gwamnatiku, ko ka na kokarin rufe alakar (Dr. Isa Ali) Pantami da ‘yan ta’adda ne?”

Wannan waka da Eidrez Abdulkareem ya fitar, ta biyo bayan martanin da ya maida wa Ministan a shafinsa na sada zumunta na zamani na Instagram kafin yanzu.

Tun jiya dubunnan mutane su na ta magana a kan wannan waka a dandalin sada zumunta na Twitter.

Kun samu rahoto cewa Fasto Ejika Mbaka ya maidawa Fadar Shugaban kasa raddi kan zargin zuwa maular kwangiloli da Malam Garba Shehu ya zarge shi da yi.

Fitaccen limamin Katolikan ya ce babu shakka ya je fadar shugaban kasa da wata manufar, ya ce ya fi karfin gori domin mutane fiye da 20, 000 su ke ci a karkashinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel