Da duminsa: Mayakan ISWAP sun kai farmaki yankin Ajiri dake Borno

Da duminsa: Mayakan ISWAP sun kai farmaki yankin Ajiri dake Borno

- 'Yan ta'addan ISWAP sun kai mugun farmaki garin Ajiri dake karamar hukumar Mafa a Borno

- Sun kai harin ne a ranar Lahadi amma har yanzu ba a san iyakar barnar da suka yi ko aka musu

- A watan Augustan da ta gabata ne 'yan gudun hijira suka koma Ajiri da taimakon gwamnatin jihar

Mayakan ISWAP, wani bangare na Boko Haram da suka rabe, a ranar Lahadi sun kai mugun farmaki yankin Ajiri dake karamar hukumar Mafa ta jihar Borno.

Harin da aka kai Ajiri ya sa an fara damuwa da halin tsaron da garin Dikwa zai shiga a kwanakin nan.

Mafa tana daya daga cikin kananan hukumomin jihar Borno da gwamnatin jihar ke ta zuba kudi domin gina gidaje saboda dawowar 'yan gudun hijira.

Har yanzu dai ba a sani ba ko an samu tsayyayun sojoji da aka tura yankin, jaridar HumAngle ta wallafa.

KU KARANTA: Ndume: Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro

Da duminsa: Mayakan ISWAP sun kai farmaki yankin Ajiri dake Borno
Da duminsa: Mayakan ISWAP sun kai farmaki yankin Ajiri dake Borno. Hoto daga @BBCHausa
Source: UGC

KU KARANTA: Buhari ya amince da karawa 'yan fansho kudi zuwa sabon karancin albashi

A kalla an samu gidaje 500 da 'yan gudun hijira suka koma a Ajiri a watan Augustan 2020 tare da taimakon gwamnatin jihar da ta samar musu da gidajen, kayan abinci da tallafin kudi.

HumAngle ta gano cewa a ranar Asabar, 1 ga watan Mayu ne dakarun sojin Najeriya suka fatattaki mayakan ISWAP da suka shiga garin Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala Balge dake da kusanci da Kamaru.

Mayakan ta'addancin sun isa a motocin yaki da babura inda aka gano cewa sun matukar jigata bayan arangamarsu da dakarun.

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta sauyawa rundunar Operation Lafiya Dole dake yakar Boko Haram suna zuwa Operation Hadin kai. Wannan ne suna na uku da aka sanyawa rundunar tun bayan kafa ta.

Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai a 2015 ya sauya mata suna daga Operation Zaman Lafiya suwa Operation Lafiya Dole, wanda yace hakan yayi shi ne domin tabbatar da cewa dole ne a samu zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

Amma Mohammed Yerima, mai magana da yawun rundunar, a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, yace sauya sunan zuwa hadin Kai na nufin zama tsintsiya daya.

Source: Legit

Online view pixel