Ndume: Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro

Ndume: Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro

- Shugaban kwamitin majalisa na kula da rundunar sojin Najeriya, Sanata Ali Ndume yace akwai bukatar kara kasafin kudin makamai

- Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta kudu, yace Najeriya bata mayar da hankali ba wurin yaki da 'yan ta'addan Boko Haram

- Ndume yace idan misali gobara ta tashi a gidan mutum, ai ba tsayawa zai yi auna wutar kashe gobarar ba, zubawa ake har ta mutu

Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazabar Borno ta kudu, yace kasafin kudi N29 biliyan da aka yi domin manyan ayyukan sojoji a 2021 ya nuna yadda Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro.

A yayin hira da gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, Ndume ya tabbatar da cewa kasashe kamarsu Chadi da Kamaru na kashe kudade masu yawa fiye da yadda Najeriya ke yi a fannin tsaro.

Ana ta kiran gwamnati da ta inganta kasafin sojin Najeriya bayan tsanantar hare-hare da 'yan ta'addan Boko Haram ke yi a yankin arewa maso gabas.

KU KARANTA: Dan majalisa ya gwangwaje mazabarsa da kyautar miliyan 50 na azumi, ya gigita jama'a

Ndume: Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro
Ndume: Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sunaye: Dubun 'yan bindigan11 dake basaja a matsayin makiyaya a Oyo ta cika

A cikin kwanakin nan ne Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasan Najeriya ya bukaci majalisar dattawa da ta kara kasafi ga rundunar domin siyan makamai.

Kamar yadda Ndume wanda shine shugaban kwamitin kula da rundunar soji a majalisar dattawa, yace Najeriya na fuskantar matsananciyar damuwa da 'yan ta'addan Boko Haram kuma hakan yasa dole a fifita fitar da kudade domin rundunar sojin.

"Idan gidanka gobara ta tashi, zaka auna ruwan da zaka kashe gobarar ne da shi? Muna cikin matsala, ballantana a yankin arewa maso gabas," yace.

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa tayi martani kan zargin da gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya jefi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shi a kan matsalar tsaro.

Ortom a ranar Talata ya zargi shugaban kasa Buhari da yi wa Fulani aiki domin su karbe Najeriya a martanin da yayi kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa wanda ake zargin makiyaya ne.

Amma kuma mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin yada labarai, Malam Garbe Shehu, ya kushe ikirarin Gwamna Ortom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel