Buhari ya amince da karawa 'yan fansho kudi zuwa sabon karancin albashi
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da karin kudin fansho zuwa sabon mafi karancin albashi
- Mukaddashin shugaban hukumar albashi na kasa, Ekpo Nta, ya sanar da hakan a ranar Juma'a a garin Kalba
- Yace za a tattaro sabon mafin karancin albashin tun daga watan Afirilun 2019 har zuwa yanzu da shugaban kasan ya amince
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin kudin 'yan fansho zuwa sabon karancin albashin kasar nan da aka duba a watan Afrilun 2019.
Ekpo Nta, mukaddashin shugaban hukumar albashi ta kasa (NSIWC) ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a garin Kalba, babban birnin jihar Cross Rivers a ranar Juma'a.
A watan Afirlun 2019, Buhari ya sa hannun kan sabuwar dokar karancin albashi. An kara daga N18,500 zuwa N30,000 a matsayin mafi karancin albashi a kasar nan.
KU KARANTA: Tsaron kasa: Buhari ya fusata, yace Ortom baya ganin laifin kansa, na wasu yake hange
KU KARANTA: Ta'addanci: Mun mayar da hankali wurin ganin bayan Boko Haram, COAS
Nta yace amincewar Buhari na nuna cewa za a karawa 'yan fansho kudi a karkashin hukumar, tun daga lokacin da aka sabunta mafi karancin albashi.
Ya ce karin kudin wanda zai fara aiki a take, za a tattaro shi ne tun daga ranar 18 ga watan Afirilun 2019, lokacin da aka saka hannu a kan dokar.
"Ina matukar farin cikin sanar da ku cewa tun bayan da shugaban kasan ya amince, takardar da ke bayyana karin a karkashin hukumar fansho ta kasa mai kwanan wata 29 ga Afirilu ta shiga hannun dukkan masu ruwa da tsaki," yace.
“Dokar sabon albashi mafi karancin da aka zartar a shekarar 2019 ya bayyana cewa karin zuwa N30,000 zai shafa dukkan ma'aikata dake karkashin tarayyar Najeriya.
"Daga nan, gwamnatin tarayya da kungiyoyi sun tattauna a kan yadda za a gyara albashi ya yi daidai da sabon mafi karancin albashi na 2019."
A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yayi kira ga alkalai a jihar da kada su kasance masu sassauci ga 'yan bindiga yayin shari'a.
Kamar yadda The Punch ta wallafa, Matawalle ya yi wannan kiran ne yayin da ya karba wasu mahukunta da ma'aikatan bangaren shari'a na jihar buda baki a gidansa dake Gusau.
"Ina kira ga alkalan dake shari'ar 'yan bindiga da su yi shari'ar cike da kishin kasa kuma ba tare da wani sassauci domin kawo karshen wannan matsalar a jihar."
Asali: Legit.ng