Da duminsa: Rundunar soji ta sauyawa Operation Lafiya Dole suna

Da duminsa: Rundunar soji ta sauyawa Operation Lafiya Dole suna

- Hukumar rundunar sojin kasan Najeriya ta sauyawa rundunar Operation Lafiya Dole suna zuwa Operation Hadin Kai

- Wannan ne karo na uku da aka sauyawa rundunar mai yakar Boko Haram suna tun bayan da aka kafa ta

- Wannan sunan yana bayyana cigaban da ake samu tare da fatan Hadin Kai a yaki da miyagun 'yan ta'addan

Rundunar sojin Najeriya ta sauyawa rundunar Operation Lafiya Dole dake yakar Boko Haram suna zuwa Operation Hadin kai.

Wannan ne suna na uku da aka sanyawa rundunar tun bayan kafa ta.

Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai a 2015 ya sauya mata suna daga Operation Zaman Lafiya suwa Operation Lafiya Dole, wanda yace hakan yayi shi ne domin tabbatar da cewa dole ne a samu zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

KU KARANTA: Baƙin mutum ya mayarwa baturiya miliyan 13 da ƴan damfara suka tura asusun bankinsa

Da duminsa: Rundunar soji ta sauyawa Operation Lafiya Dole suna
Da duminsa: Rundunar soji ta sauyawa Operation Lafiya Dole suna. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sunaye: Dubun 'yan bindigan11 dake basaja a matsayin makiyaya a Oyo ta cika

Amma Mohammed Yerima, mai magana da yawun rundunar, a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, yace sauya sunan zuwa hadin Kai na nufin zama tsintsiya daya.

Hakan yana daga cikin kokarin Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasan, na ganin an kakkabe duk wani rashin hadin kai dake wurin kuma a samar da aiki cike da kwarewa.

"Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru, ya amince da sauya suna Operation Lafiya dole zuwa Operation Hadin kai," takardar tace.

“An yi hakan ne saboda tsabar cigaban da rundunar sojin kasar ta samu a shekarun da suka gabata kuma saboda a tabbatar da hakan."

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa tace Ejike Mbaka, shugaban Adoration Ministry (AMEN), ya taba kawai shugaban kasa 'yan kwangila uku amma aka dakatar da shi.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace Mbaka ya makance da har ya bukaci shugaban kasa ya yi murabus sakamakon tsanantar matsalar tsaro a kasar nan.

A wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, Shehu yace akwai matukar abun mamaki ta yadda wanda ya goyi bayan shugaban kasan har sau biyu a yau ya sauya ya koma yana neman yayi murabus ko a tsige shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng