Gwamna Zulum Ya Miƙa Gwamnatin Jihar Borno Ga Usman Kadafur
- Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya mika gwamnatin jihar ga mataimakinsa Usman Kadafur
- Zulum ya mika gwamnatin na tsawon kwana 21 ga Kadafur ne domin ya samu daman zuwa hutu
- Gwamna Zulum ya umurci dukkan ma'aikatan gwamnati da hukumomi a jihar su bada cikaken hadin kai bisa mika mulkin
Majalisar dokokin jihar Borno ta amince mataimakin gwamnan jihar Umar Usman Kadafur ya yi aiki a matsayin gwamna na rikon kwarya daga ranar 29 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Mayun 2021.
Hakan na zuwa ne sakamakon hutu na kwanaki 21 da Gwamna Babagana Zulum zai tafi kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar a shafinta na Twitter.
DUBA WANNAN: Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina
Kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarin Lawan ne ya sanar da amincewar majalisar a wasika mai dauke da kwanan wata na 26 ga watan Afrilu.
Zulum ya rubutu wasikar neman samun amincewar majalisar ne a ranar 23 ga watan Afrilun 2021 domin ya samu ya tafi hutun kwanaki 21.
Sashi na 190 (1) na kudin tsarin mulki ya bukaci gwamnan ya nemi izinin majalisar dokokin domin nada mataimakin gwamna ya yi aiki a matsayin gwamna na rikon kwarya domin ya samu ikon gudanar da mulki a jihar ba tare da ya tuntubi gwamna ba.
KU KARANTA: An Harbe Auwalu Daudawa Har Lahira Kwana Huɗu Bayan Komawarsa Daji
"Gwamnan ya umurci dukkan ma'aikatan gwamnati da hukumomi su bada cikaken hadin kai bisa mika mulkin da ya yi ga mataimakinsa," a cewar kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau.
A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.
Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.
Asali: Legit.ng