Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina

Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina

- An kama wani matashi da ya saci wayoyin salula 273 da kudinsu ya kai N15m a Katsina

- Yan sanda sun ce ya kutsa gidan wani ne ya sace wayoyin salular daga cikin motansa

- Da zarar an kammala bincike za ta gurfanar da wanda ake zargin a kotu a cewar yan sandan

Yan sanda a jihar Katsina, a ranar Juma'a sun kama wani tsohon mai laifi da wayoyin salula na sata guda 273 da kudinsa ya nai Naira miliyan 15, Premium Times ta ruwaito.

Kakakin yan sandan, Gamba Isah, ya ce wanda ake zargin, Ibrahim Lawan, dan shekara 23, mazaunin Fegi Quaters a karamar hukumar Daura ya kutsa cikin mota ne ya sace wayoyin.

DUBA WANNAN: 2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC

Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina
Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina. Hoto: @PremiumTimesNg
Asali: Twitter

Yan sandan sun ce a ranar 22 ga watan Afrilu aka sace wayoyin amma bayan an shigar musu da korafi, yan sandan suka yi nasarar kama wanda ake zargin.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kori Ma'aikata Da Ba Su San Makamashin Aiki Ba

"Wanda ake zargin da ake kira 'Abba Kala' (Abba Swags) hatsabibin barawo ne, tsohon mai laifi, wanda ya saba da shiga gidan mutane yana sata da kuma satan babur," in ji yan sandan.
"Dubunsa ta cika yayin da wanda ake zargin ya kutsa gidan wani Kamalu Ibrahim, dan shekaru 33, mazaunin Shagari Low Cost, Daura, ya balle motarsa, BMW 3 Series mai lamba JW 01 DRA ya sace wayoyin.
"An gano dukkan wayoyin 273 da ya sace a tare da shi a yayin da yan sanda ke bincike.
"Wanda ake zargin ya amsa laifinsa a hannun yan sanda. Za a gurfanar da shi da zarar an kammala bincike," in ji kakakin yan sandan.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel