2023: An Ƙaddamar da Ƙungiyar Goyon Bayan Saraki a Daura

2023: An Ƙaddamar da Ƙungiyar Goyon Bayan Saraki a Daura

- An kaddamar da kungiyar matasa masu goyon bayan Bukola Saraki ya yi takarar shugaban kasa a 2023

- Abubakar Nuhu Adam, shugaban kungiyar ya ce suna goyon bayan Saraki ne saboda irin ayyukan da ya yi wa matasa

- Adam ya kuma ce ya zabi kaddamar da kungiyar a Daura ne saboda nan ne garinsa kuma don nuna wa duniya rashin jin dadin halin da kasar ke ciki

Wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

2023: An ƙaddamar da ƙungiyar goyon bayan Saraki a Daura
2023: An ƙaddamar da ƙungiyar goyon bayan Saraki a Daura. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

"Mun yanke shawarar cewa za mu goyi bayan wanda ke son cigaban matasa kuma Sanata Saraki ne kadai ya cika wannan ka'idar.

"Dukkanmu mun san rawar da ya taka don ganin an aiwatar da dokar Not Too Young To Run a Majalisar Tarayya a lokacin yana shugaban majalisa.

"Mun kuma san cewa shine kadai mamba na kwamitin zartarwa na kasa na PDP daya dage cewa dole jam'iyyar ta tallafawa matasa sannan ya goyi bayan matasa su iya yin takara a jam'iyyar," in ji shi.

KU KARANTA: Dangote da Alakija sun shiga jerin ƴan Nigeria da suka fi kyauta a 2021

Hon Adam ya kuma ce tsohon gwamnan na jihar Kwara ya dauki nauyin dubban matasa domin su kara karatu a jami'o'i daban-daban a duniya.

Kazalika, shugaban kungiyar ya ce sun zabi kaddamar da kungiyar a Daura ne saboda nan ne karamar hukumarsa kuma domin su nuna wa duniya rashin gamsuwarsu da halin da kasar ke ciki yanzu.

Daura ce garin Shugaban Nigeria mai ci a yanzu, Muhammadu Buhari.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164