An Harbe Auwalu Daudawa Har Lahira Kwana Huɗu Bayan Komawarsa Daji

An Harbe Auwalu Daudawa Har Lahira Kwana Huɗu Bayan Komawarsa Daji

- Auwalu Daudawa, shugaban yan bindiga wanda ya jagoranci sace daliban makarantar sakandare ta Kankara su 300 a Katsina ya mutu

- Daudawa ya gamu da ajalinsa ne kimanin kwanaki hudu bayan ya yi watsi da afuwar da gwamnati ta masa ya koma daji

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan wasu tawagar dan bindiga mai suna Ballolo ne suka bindige Daudawa har lahira yayin da ya tafi daukan fansa

An kashe hatsabibin dan bingida Auwalu Daudawa da aka fi sani da sace dalibai fiye da 300 daga makarantarsu da ke Kankakara a jihar Katsina.

Daily Trust ta ruwaito cewa an bindige shi yayin fada tsakaninsa da wasu kungiyar yan bindigan a yammacin ranar Juma'a a dajin Dumburum da ke tsakanin karamar hukumar Zurmi a Zamfara da Batsari a jihar Katsina.

An harbe Auwalu Daudawa har lahira kwana hudu bayan komawarsa daji
An harbe Auwalu Daudawa har lahira kwana hudu bayan komawarsa daji. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne kwanaki hudu bayan Daudawa ya koma daji ya yi watsi da afuwar da gwamnatin Zamfara ta masa.

DUBA WANNAN: 2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC

Daudawa ya shahara ne bayan ya tsara hari da sace dalibai fiye da 300 daga Makarantar Sakandare da ke Kankara a jihar Katsina.

Watanni biyu bayan sace daliban, Daudawa ya isa Gusau babban birnin jihar Zamfara tare da mutum biyar yan tawagarsa inda ya sanar da cewa ya tuba sannan ya mika wa yan sanda AK-47 fiye da 20 da wasu makamai.

A ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito cewa Daudawa ya koma daji bayan barin sabon gidansa da ke Damba a wajen garin Gusau.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ce an kashe Daudawa ne yayin da shi da yaransa suka kaiwa wasu yan bindiga da ke biyaya ga wani dan bindiga mai suna Ballolo harin ramuwar gayya.

KU KARANTA: Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina

An gano cewa Ballolo da yaransa sun kai wa yan tawagar Daudawa hari sunyi yunkurin sace shanunsu inda suka kashe biyu cikinsu a lokacin Daudawa yana Gusau bayan ya tuba.

Daudawa ya sha alwashin sai ya dauki fansa.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa yaran Ballolo sun bindige Daudawa a yayin da suka tafi daukar fansar duk da cewa suma sun kashe wasu daga cikin yaran Ballolo.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel