Da Ɗuminsa: An Samu Sauƙin Ta’addanci Tun Hawan Buhari Mulki a 2015, Gwamna Fayemi

Da Ɗuminsa: An Samu Sauƙin Ta’addanci Tun Hawan Buhari Mulki a 2015, Gwamna Fayemi

- Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya ce ta'addanci ya yi sauki a Nigeria tun bayan da APC ta karbi mulki a 2015

- Fayemi ya yi wannan tsokacin ne a wurin wani taro da wata coci ta shirya ranar Asabar Legas

- Fayemi ya ce abin da yasa tsaro ya sake tabarbarewa a baya bayan nan shine yawaitar makamai da rashin tsaro a iyakokin Nigeria

Shugaban kungiyar gwamnonin Nigeria kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce ta'addanci ya yi sauki a Nigeria tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulki a 2015, The Punch ta ruwaito.

Tsohon ministan ya ce kowa na rayuwa cikin tsoro duk da cewa jam'iyyar da ke mulki a kasar ta samu nasarori kan yaki da ta'addanci amma akwai bukatar ta kara jajircewa.

DUBA WANNAN: An Harbe Auwalu Daudawa Har Lahira Kwana Huɗu Bayan Komawarsa Daji

Da Ɗuminsa: An Samu Sauƙin Ta’addanci Tun Hawan Buhari Mulki a 2015, Gwamna Fayemi
Da Ɗuminsa: An Samu Sauƙin Ta’addanci Tun Hawan Buhari Mulki a 2015, Gwamna Fayemi. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

Fayemi ya yi magana ne a ranar Asabar yayin taron shekara-shekara da babban faston cocin Covenant Christian Centre, Poju Oyemade ya shirya a Legas.

Da farko Fayemi ya ce ba zai yi tsokaci ba kan yadda ya ke kallon kamun ludayin gwamnatin jam'iyyar APC a kasar ba amma daga baya ya yi tsokaci kamar haka:

"A 2015, mun yi alkawurra da yawa amma alkawarin da ya fi daukan hankalin mutane shine gaskiya da rikon amana."
"Wasu da dama ba za su yarda da ni ba amma a batun ta'addanci mun samu sauki idan aka kwatanta da 2015 a lokacin da muka karbi mulki.
"Ka tuna da bam da aka saka a gidan Majalisar Dinkin Duniya, coci-coci da aka kona a Abuja, ana tsoron zuwa Abuja a lokacin da Arewa maso Gabas amma an samu sauki a shekaru hudu na mulkin Buhari."

KU KARANTA: Da Taimakon Ƴan Sintiri, Maiduguri Ta Fi Abuja Tsaro, Gwamna Zulum

Gwamnan ya ce ta'addancin ya sake dawowa saboda yaduwar makamai da matsalolin kan iyakokin Nigeria da ma rasuwar Shugaban Chadi Idriss Deby.

Ya kara da cewa gwamnatin Buhari da APC tana duk mai yiwuwa domin ganin ta kare rayuka da dukiyoyin yan Nigeria.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel