Da Taimakon Ƴan Sintiri, Maiduguri Ta Fi Abuja Tsaro, Gwamna Zulum
- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya ce a halin yanzu Borno ta fi Abuja tsaro
- Zulum ya ce jihar ta cimma wannan nasarar ne ta hanyar amfani da 'yan sintiri wurin samar da tsaro
- Zulum ya ce tuni har yan sintirin sunyi nasarar fatattakan 'yan ta'adda sun koma dajin Sambisa
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Juma'a ya ce yana amfani da yan sintiri/ 'yan sakai wurin magance kallubalen tsaro da jiharsa ke fama da su, Vanguard ta ruwaito.
Zulum ya yi furta hakan na a Owerri, a lokacin da ya karbi wasikar gayyata domin bashi lambar yabo na shugabanci da kungiyar yan jaridar Nigeria, NUJ, reshen jihar Imo ta aika masa.
DUBA WANNAN: Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina
Emma Odibo, sakataren NUJ na jihar Imo ne ya gabatar da wasikar a madadin shugaban kungiyar Chris Akaraonye.
Zulum wanda ya samu wakilcin babban mai taimaka masa na musamman a bangaren watsa labarai, Baba Shaikeh Haruna, ya ce yan sakai na cikin matakan da gwamnatin Zulum ta dauka domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma.
KU KARANTA: 2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC
A cewar Zulum: "Mu a Borno sun shafe shekaru 12 muna fama da kallubalen tsaro, sai dai abubuwa da yawa sun canja cikin matakan da muka dauka shine amfani da yan sintiri domin samar da tsaro a jihar; su ke samar da tsaro a jihar har sun fatattaki yan ta'adda zuwa dajin Sambisa.
"Idan ka zo Maiduguri, za ka yi mamaki, har ya fi Abuja tsaro. Wasu lokutan yadda mutane ke magana kan batun tsaro a Borno, ba haka za ka gan shi ba idan ka zo jihar."
A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.
Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.
Asali: Legit.ng