Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Domin Murnar Ranar Ma’aikata

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Domin Murnar Ranar Ma’aikata

- Ma’aikatan Najeriya za su bi sahun sauran kasashen duniya don bikin ranar ma’aikata ta 2021

- Domin murnar ranar, gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin, 3 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga jama'a

- Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya taya ma'aikatan Najeriya murna tare da bukatan su da su kara jajircewa

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 3 ga watan Mayu, 2021 a matsayin hutu domin bikin ranar ma’aikata ta duniya ta bana.

Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya yi sanarwar a madadin Gwamnatin Tarayya, ya taya ma’aikatan Najeriya murna saboda shaida bikin na bana, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Abun Ya Kayatar: Hotunan DCP Abba Kyari Yana Tuka Babur Akan Titi Ba Tare da Tsaro Ba

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Domin Murnar Ranar Ma’aikata
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Domin Murnar Ranar Ma’aikata Hoto: @ravetvchannel
Asali: Twitter

Ya yaba musu kan haƙuri, fahimta da goyan baya da suke bayarwa wajen tafiyar da manufofi da shirye-shiryen mulkin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari na kai kasar zuwa ga mataki na gaba.

Aregbesola a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis daga Babban Sakataren Ma’aikatar Cikin Gida, Shuaibu Belgore, ya yi kira ga ma’aikatan Najeriya da kungiyoyin kwadago da su kara himma da kishin kasa, yana mai cewa “matsalolin da ake ciki a yanzu zai wuce ba da dadewa ba saboda gwamnati ta himmatu wajen tsaron rayuka da dukiyoyin yan Nijeriya duka.”

An yi wa sanarwar take da, ‘FG ta bayyana ranar Litinin, 3 ga watan Mayu, 2021 hutu don bikin ranar ma’aikata 2021.

Ministan ya kara da cewa, “Gwamnati na sanya dukkan dabaru don dakile matsalolin rashin tsaro a kasar. Don haka ina kira ga kungiyar kwadago da dukkan ‘yan kasa masu kishin kasa da su jajirce matuka a kokarin ganin bayan rashin tsaro."

KU KARANTA KUMA: Boko Haram Ta Kai Hari Kan Sansanin Soji A Borno, Ta Lalata Komai, Cewar Rahoto, Sojoji Sun Maida Martani

Aregbesola ya yiwa daukacin ma’aikatan Najeriya fatan yin bikin cikin zaman lafiya.

A wani labari na daban, an kama wasu ma'aikatan gwamnati da aikata fashi da makami a Zamfara, a cewar Gwamnatin Jihar, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya sanya wa hannu a ranar Laraba, ma'aikatan gwamnatin suna daga cikin 35 da aka kama kuma ake zargin 'yan bindiga ne a Gusau, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng