Abun Ya Kayatar: Hotunan DCP Abba Kyari Yana Tuka Babur Akan Titi Ba Tare da Tsaro Ba

Abun Ya Kayatar: Hotunan DCP Abba Kyari Yana Tuka Babur Akan Titi Ba Tare da Tsaro Ba

- Mataimakin kwamishanan yan sanda Abba Kyari ya sa mutane fadin albarkacin bakunansu a shafukan sada zumunta kan hotunan shi yana tuka babur

- Kanin Abba mai suna Muhammed Kyari ne ya wallafa hotunan a shafin Facebook

- Ya birge masu amfani da shafukan sada zumunta matuka saboda gaskiyar cewa mataimakin kwamishanan 'yan sandan ya dauki rayuwa da sauki

Mataimakin kwamishanan ‘yan sanda Abba Kyari ya haifar da da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan hotunan shi yana tuka babur sun bayyana a yanar gizo.

A cikin hotunan da kaninsa Muhammed Kyari ya wallafa a Facebook, an ga dan sandan yana tuka babur a lokuta biyu mabanbanta.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram Ta Kai Hari Kan Sansanin Soji A Borno, Ta Lalata Komai, Cewar Rahoto, Sojoji Sun Maida Martani

Abun Ya Kayatar: Hotunan DCP Abba Kyari Yana Tuka Babur Akan Titi Ba Tare da Tsaro Ba
Abun Ya Kayatar: Hotunan DCP Abba Kyari Yana Tuka Babur Akan Titi Ba Tare da Tsaro Ba Hoto: Mohammed Kyari
Asali: Facebook

A ɗaya daa cikin hotunan, an gano shi zaune shi kaɗai a kan babur din. Dayan hoton kuma ya nuno shi yana ragewa wani mutumi hanya.

Jami'in dan sandan ya wallafa hotunan a shafinsa sannan masu amfani da Facebook sun mamaye sashen sharhin nasa tare da martani masu dadin ji.

KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Abubuwa Na Kara Tabarbarewa a Kasar, Inji Dan Majalisa Na APC

Mala Mohammed Garba ya ce:

"Wannan shi ne ya sa shi zama na daban, saukin kansa."

Salihu Mohammed Chado ya yi sharhi:

"Babu wani sharri da zai iya samunsa. Kullum kariyar Allah tana tare da shi."

Kennedyjohnsyn Obinna ya rubuta:

"Wannan na nufin shi mutum ne mai saukin kai."

Hotunan dai ba su burge Sheikh Sheikh ba. Ya rubuta:

"Ba abin burgewa ko kaɗan. Ya kamata ya mai da hankali sosai kuma ya guji maganganun yaudara don kawai ya hau babur.

"Wannan ba saukin kai ba ne illa wauta."

A wani labarin, hukumar tsaron farin kaya DSS ta ce yan kungiyar IPOB da hukumar tsaron da suka kafa ESN sun sayi bama-bamai da suke niyyar tayar da tarzoma da su a jihar Imo.

Hukumar ta ce ta samu labarin leken asiri cewa yanzu haka ana tafiyar da bama-baman dake jihar Legas zuwa karamar hukumar Orlu, a jihar Imo, The Punch ta ruwaito.

DSS ta bayyana hakan ne a wasikar da ta aikewa Kwamandan Artillery Brigade, Obinze, Owerri, Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng