Boko Haram Ta Kai Hari Kan Sansanin Soji A Borno, Ta Lalata Komai, Cewar Rahoto, Sojoji Sun Maida Martani
- Wasu yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba sun sake rasa rayukansu saboda rashin tsaro
- Wannan ya biyo bayan wani rahoton harin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai kan sansanin sojoji a Borno
- A cewar rahoton, kimanin mutane 50 ne suka bata bayan harin
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa kimanin Sojoji 18 ne suka rasa rayukansu bayan ‘Yan Boko Haram sun kai hari sansanin su da ke Bono.
Jaridar ta ruwaito cewa a kalla babban jami’in soja guda da sojoji 17 sun mutu a arangamar.
KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Abubuwa Na Kara Tabarbarwewa a Kasar, Inji Dan Majalisa Na APC
Sai dai, rundunar a yayin da take tabbatar da harin a wata sanarwa da ta wallafa a Facebook ta ce jami’i daya ne kawai da sojoji shida suka mutu, inda ta kara da cewa jami’anta sun yi nasarar dakile harin.
A halin da ake ciki, kafar yada labaran ta ambato wasu majiyoyin soja sun ce matsayin rundunar sojojin ba gaskiyar abin da ya faru ba ne.
Kafar watsa labaran ta ci gaba da ikirarin cewa kimanin wasu sojoji 43 sun samu munanan raunuka yayin da wasu jami’ai 50 suka bace.
Ta kara da cewa an lalata sansanin sojan da abin ya shafa, hedikwatar bataliya ta 156 a Mainok gaba daya.
An ce 'yan ta'addan sun kuma kwashe makamai da alburusai, sun ƙone duk abin da ke wurin.
KU KARANTA KUMA: Garuruwan Jihar Neja Sun Tattauna Da ’Yan Fashi Domin Tsagaita Wuta
A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Binuwai tace jami'anta sun halaka 'yan bindiga uku yayin samamen da suka kai sansaninsu a ranar Laraba.
Catherine Anene, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, tace 'yan sandan sun samu miyagun makamai kamar su AK-47, harsasai, wukake, adduna da kuma layu.
Kamar yadda takardar da kakakin 'yan sandan ta fitar ta nuna, sansanin 'yan bindigan na rufe ne a dajin Tomatar Imande dake karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar.
Asali: Legit.ng