Allah Ya Yi Wa Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma Rasuwa a Kano

Allah Ya Yi Wa Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma Rasuwa a Kano

- Alhaji Abdullahi Dantalata Karo, mataimakin karamar hukumar Ungoggo ya riga mu gidan gaskiya

- Injiniya Abdullahi Garba Ramat, shugaban karamar hukumar Ungoggo ne ya bada sanarwar a ranar Litinin

- Majiyoyi sun tabbatar da cewa za a yi jana'izarsa a yau Litinin a Kano bisa koyarwar addinin musulunci

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Ungoggo a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Dantalata Karo ya riga mu gidan gaskiya.

Shugaban ƙaramar hukumar, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ne ya sanar da rasuwar a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.

DUBA WANNAN: El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

Allah Ya Yi Wa Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma Rasuwa a Kano
Allah Ya Yi Wa Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma Rasuwa a Kano. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Sakon na Facebook ya ce, "Daga Allah muka fito kuma gare shi zamu koma! Allah ya jiƙan Abdullahi Dantalata Karo (Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Ungoggo). Allah ya yafe masa kurakuransa, ya bawa iyalansa haƙuri da juriyar rashinsa, Allah ya ƙara mana gaskiya da imani."

Sai dai, sanarwar tasa ba ta bayyana abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba, rahotanni sun ce za a yi jana'izarsa yau a Kano.

KU KARANTA: Lalong da Onaiyekan Sun Ziyarci Cibiyar Musulunci Yayin Azumi Don Bada Gudunmawa

Kafin rasuwarsa, Alhaji Karo ne mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Ungoggo kuma tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a ƙaramar hukumar.

Ya yi takarar shugaban ƙaramar hukuma kafin ya kuma amince ya yi takarar mataimakin shugaban ƙaramar hukuma.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel