Lalong da Onaiyekan Sun Ziyarci Cibiyar Musulunci Yayin Azumi Don Bada Gudunmawa

Lalong da Onaiyekan Sun Ziyarci Cibiyar Musulunci Yayin Azumi Don Bada Gudunmawa

- Cardinal Onaiyekan da Gwamna Lalong na jihar Plateau sun ziyarci cibiyar musulunci na Al-Habibiyya da ke Abuja

- A yayin ziyarar da suka kai a lokacin shan ruwa, gwamnan da malamin addinin kiristan sun raba wa mutane kayan abinci

- Shugaban cibiyar, Fuad Adayemi ya ce ziyarar da su gwamnan suka kawo abin koyi ne da ke nuna halayensu a matsayin shugabanni masu son zaman lafiya

Gwamnan jihar Plateau da John Cardinal Onaiyekan sun ziyarci cibiyar musulunci ta Al-habiyya da ke Guzape a babban birnin tarayya Abuja domin bada gudunmawa, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na cikin tsarin bada tallafin da babban malamin addinin kiristan ya saba bawa musulmi a duk shekara.

Lalong da Onaiyekan Sun Ziyarci Cibiyar Musulunci Yayin Azumi Don Bada Gudunmawa
Lalong da Onaiyekan Sun Ziyarci Cibiyar Musulunci Yayin Azumi Don Bada Gudunmawa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Makut Macham ya fitar a garin Jos.

DUBA WANNAN: El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

Lalong ya jinjinawa malamin addinin kiristan saboda nuna kauna ga musulmi da wasu masu addinan daban.

Gwamnan wanda ya yi wa Onaiyekan rakiya cibiyar yayin shan ruwa a ranar Juma'a ya ce hakan abin koyi ne kuma yana iya rage zargi da kiyayya tsakanin musulmi da kirista.

Ya ce irin wannan alakar tsakanin musulmi da kirista na iya habbaka zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu.

Daya bisani, Onaiyekan ya mika godiyarsa ga cibiyar ta Al-habibiyya domin gayyatarsa da ta ke yi.

Ya ce duk da tada rikici da tsiraru ke yi, mutanen Nigeria masu son zaman lafiya ne duk da banbancin addini da ke tsakaninsu.

KU KARANTA: ‘Muna da Ƙarfin Murƙushe Ku’, Buhari Ya Gargaɗi Ƴan Bindiga Kan Kisar Mutum 83 a Zamfara

Ya gargadi yada maganganun da ke nuna cewa yan Nigeria na yaki da juna wanda hakan ba gaskiya bane.

Limanin cibiyar musuluncin ta Al-habibiyya, Fuad Adayemi ya ce ziyarar da su gwamnan suka kawo abin koyi ne da ke nuna halayensu a matsayin shugabanni masu son zaman lafiya.

Shugaban NDLEA, Buba Marwa shima ya hallarci taron shan ruwan inda gwamna Lalong da Onaiyekan suka raba wa mutane gudunmawar kayan abinci.

An kuma yi addu'ar samun zaman lafiya a Nigeria.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel